Yawon Buɗe Ido

Zanzibar ta kafa Tarihi a Yawon buɗe Ido

Zanzibar na ci gaba da ƙarfafa matsayin ta a fannin Yawon buɗe Ido a Afirka, inda matakan Gwamnati da shirye-shiryen haɗin guiwa ke haifar da tabbataccen ci gaba mai ɗorewa.

Tsibirin Zanzibar da ke cikin ƙasar Tanzaniya ya kafa sabon tarihi a fannin Yawon buɗe Ido, inda aka karɓi masu yawon buɗe ido 106,108 a cikin watan Yuli, 2025 — mafi yawan adadi da aka taɓa samu cikin wata guda a tarihin tsibirin, a cewar Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Zanzibar (ZCT).

Wannan adadi ya zarce duk wasu ƙididdiga da aka samu a baya-bayan nan, inda yake tabbatar da ci gaban Zanzibar a matsayin babban wuri mai jan hankalin masu Yawon buɗe Ido daga ko’ina cikin Duniya.

   Ƙididdiga

Rahotanni daga ZCT sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Yuli na shekarar 2025, jimillar masu Yawon buɗe Ido da suka isa Zanzibar ya kai 476,875.

Idan aka kwatanta da shekarar 2023, inda aka samu jimillar 548,503 cikin shekara ɗaya, da kuma haɓakar kashi 42.4% da aka samu daga Janairu zuwa Oktoba na 2022, wannan sabon ci gaba na 2025 ya nuna ci gaba mai karfi da gagarumar nasara.

                     Bayanin Hukuma

A cewar Sakataren Zartarwa na Hukumar, Mista. Arif Abbas Manjo, wannan gagarumin ci gaban ya samo asali ne daga haɗin guiwar Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wajen; faɗaɗa filin tashi da saukar jiragen sama na Abeid Amani Karume, da Inganta tashar Jiragen Ruwa, da hanyoyin sufuri, sauye-sauyen dokoki, da manufofi masu sassauci, da kuma ƙara ƙaimi wajen sabbin tallar kasuwanci na Yawon buɗe Ido.

filin tashi da saukar jiragen sama na Abeid Amani Karume

Tashar Jiragen ruwa na Zinzabar

“Mun ga sauye-sauye masu muhimmanci a wuraren shigowa da ficewa, da kuma ayyukan ci gaba da sabunta tsarin sadarwa, wanda ya taimaka ƙwarai wajen karɓar baƙi da yawa a wannan lokaci,” in ji Manjo.

Sakataren Zartarwa na hukumar Yawon Buɗe Ido ta Zanzibar, Mista. Arif Abbas Manjo

        Tattalin Arziki da Ƙalubale

Yawon buɗe Ido na taka rawa mai muhimmanci a tattalin arzikin Zanzibar.

Wasu masu Yawon buɗe ido a Tsibirin Zanzibar

Ya na bayar da:

  • Ayyukan yi ga dubban mutane
  • Samar da kuɗaɗen shiga
  • Faɗaɗa kasuwanni da kamfanoni masu zaman kansu

Sai dai, masana sun nuna damuwa, cewar, wannan ƙaruwar maziyarta na iya haifar da:

  • Matsi a kan ababen more rayuwa kamar; ruwa, lantarki da hanyoyi
  • Matsalolin ƙarancin muhalli, dss.

       Martanin Masu Ruwa da Tsaki

Wasu masu gudanar da Otal-Otal sun bayyana cewa, a cikin watan Yuli, buƙatar masauki da ayyukan Yawon buɗe Ido ya haura ƙima, inda Otal-Otal da dama ke aiki ba-ji-ba-gani (100%).

Wata kasuwar rairayin bakin Teku

Wannan ya jaddada buƙatar:

  • Ƙarin saka jari
  • Inganta tsarin masauki
  • Faɗaɗa hanyoyin sadarwa don biyan buƙatun baƙi

                  Hasashen Gaba

Kodayake, hukumar ba ta fitar da hasashen shekara-shekara ba tukuna, ana sa ran za a samu ƙarin yawan baƙi, yayin da ake tunkarar kakar Yawon buɗe Ido ta ƙarshen shekara (Nuwamba – Disamba), wadda ke ɗaya daga cikin lokutan da ke jawo baƙi da dama.

Wannan ci gaba ya nuna yadda Zanzibar ke ƙara shahara a idon Duniya, a matsayin ɗaya daga cikin fitattun wuraren Yawon buɗe Idon a nahiyar Afirka.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Yawon Buɗe Ido

Madyan: Garin Annabi Shu’aib (AS)

Madyan, garin mutanen Annabi Shu’aib AS, ya na nan a Al-Bada’a, yankin Tabuk a Arewa maso Yammacin ƙasashen Larabawa a
Yawon Buɗe Ido

Obudu Mountain Resort: Shahararren Wurin Shaƙatawa a Najeriya

Tsaunin Obudu, (wadda a da ake kira da Obudu Cattle Ranch), wani kwari ne a rafin Oshie na tsaunukan Sankwala,