Gwamnatin Netherlands ta mayar wa Najeriya kayayyakin tarihi 199 da aka sace
BY Salahuddeen Muhammad
06/08/2025
Gwamnatin ƙasar Netherland ta mayar wa Najeriya wasu kayayyakin tarihi 119 da aka sace lokacin da Birtaniya ta ci Daular Benin da yaƙi a 1897.
Waɗannan na ɗaya daga cikin kayayyaki mafiya yawa da aka mayar wa Najeriya tun bayan mamaye tsohuwar Daular.
Netherlands za ta mayar wa Najeriya kayan tarihi da Turawan Mulkin Mallaka suka sace https://is.gd/eCIc3x
Kayayyakin da aka mayar dai sun haɗa da; wani tsuntsu na Tagulla, da kan mutum-mutumi na Ice, da kuma mutum-mutumin wani jarumin Sarki da aka yi da Tagulla da Zakara da dai sauransu.
An dai kawo kayan tarihin na Daular Benin ɗin ne daga Gidan adana kayan tarihi na Wereland da ke ƙasar ta Netherlands.
Haka nan, an yi bikin miƙa kayayyakin a hukumance a jihar Legas, an kuma miƙa wasu daga cikin kayayyakin ga Oba na Benin a birnin Benin, a wani mataki na an nuna mayar da kayan zuwa tushensu.
Da yake karɓar kayayyakin daga tawagar gwamnatin Netherlands, basaraken ya ce, mayar da kayan tarihin ga masarautar wata muhimmiyar nasara ce ta fuskar hulɗar diflomasiyya da ta al’adu tsakanin Netherlands da Najeriya.
Ministar fasaha da al’adu ta Najeriya Hannatu Musa Musawa, wadda ta rattaba hannu kan kundin yarjejeniyar miƙa ababen tare da Jakadan ƙasar Netherlands mai kula da harkokin al’adu na ƙasa da ƙasa, Dewi Van de Weerd.
“Najeriya na ƙoƙarin alkinta ababen tarihinta da al’adunta,” in ji Hannatu.
Ita kuwa jagorar tawagar kana shugabar gidan tarihin na Wereland, Ms. Marieke Van Bommel, ta jaddada manufar gwamnatin ƙasarta ta mayar da dukkanin kayan tarihin da aka sata zuwa inda aka sato su, in da ta ce, ƙasarta ta kwashe shekaru fiye da 100 ta na ajiye da waɗannan kayayyakin na Benin guda 119 da suka mayar.
An dai yi bikin miƙa kayayyakin ne a babban Gidan adana kayan tarihi na Ƙasa da ke Legas a gaban idon wakilan gwamnatocin ƙasashen biyu da kuma na Masarautar Benin ɗin.