Kaso 40% na Yaran Najeriya na Fama da Cutar Rashin Girma – NDHS
BY Salahuddeen Muhammad
26/02/2026
0
Comments
20 Views
Sabbin bayanai daga Nigeria Demographic and Health Survey (NDHS), waɗanda aka tattara daga ƙarshen shekarar 2023 zuwa farkon shekarar 2024, sun nuna cewa, kimanin kashi 40 cikin 100 na Yaran Najeriya da ke ƙasa da shekaru biyar su na fama da rashin girma (stunting), alamar ƙarancin gina jiki na dogon lokaci wanda ke iya shafar ci haɓakar jiki da Ƙwaƙwalwa.
Mene ne Stunting?
“Stunting” na nufin Yaro ba ya girma daidai da shekarunsa sakamakon rashin isasshen Abinci mai gina jiki (Tamowa) na tsawon lokaci. Masana sun ce, wannan yanayi na iya shafar bunƙasar Ƙwaƙwalwa, koyo da lafiyar jiki, kuma ba ya dawowa idan ba a yi magani da wuri ba.
Muhimman Ƙididdiga
Kimanin 40% na yara masu ƙasa da shekaru biyar su na fama da ‘Stunting’
Kusan 8% su na ‘wasted’ (rashin nauyin gaggawa)
Kusan 27% su na ‘underweight’ (rashin nauyi)
Wannan ya nuna cewa, yanayin Abinci da lafiyar Yara bai inganta sosai a cikin shekaru da suka gabata ba, musamman a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Su waye suka bayyana haka?
A taron Ƙasa kan abinci da tsaron abinci a Abuja:
Kashim Shettima, Mataimakin Shugaban Najeriya, ya bayyana cewa matsalar cutar ‘stunting’ ta na shafar kusan Yara huɗu cikin 10 a ƙasa da shekaru biyar.
“Ba za mu iya magance talauci da bunƙasa tattalin arziki ba idan ba mu fara da kare lafiyar yaranmu tun daga shekarun farko ba.”
Ali Pate, Ministan Lafiya, ya jaddada cewar ‘stunting’ ba wai matsalar girman jiki kaɗai ba ce, illa ce ga bunƙasar Ƙwaƙwalwa da ƙarfin koyon ababe daga Yara.
Ali Pate, Ministan Lafiya
Shugaban Hukumar Abinci da Gina Jiki ta ƙasa (Nutrition Department) ya ƙara bayyana cewa, hauhawar farashin Abinci sun ƙara tsananta matsalar.
Mrs. Ladidi-Bako Aiyegbusi, shugabar hukumar Abinci da gina jiki ta ƙasa
Dalilan Matsalar
Masana sun bayyana cewa, ‘stunting’ ya na faruwa ne saboda abubuwa kamar:
Talauci da rashin wadataccen abinci mai gina jiki
Rashin sanin ilimin abinci mai kyau ga iyaye
Rashin ruwa mai tsafta da kulawar lafiya
Farashin kayan Abinci mai yawa
Rikici da yanayi a wasu yankuna
Illolin Stunting
Rashin bunƙasar Ƙwaƙwalwa da koyo
Rauni ga jiki da ƙarancin ƙarfi
Matsaloli wajen aiki da karatu a gaba
Matakan Da Ake Ɗauka
Gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu su na ƙoƙarin:
Ƙaddamar da shirye‑shirye irin su “Nutrition 774 Initiative”
Inganta ilimin Abinci mai gina jiki da shayarwa
Haɗin kai da hukumomin ƙasa da ƙasa don ƙarin tallafi
Masana sun yi gargadi cewar, rashin ɗaukar matakan gaggawa zai iya jefa ƙasar cikin mummunan yanayin lafiya da tattalin arziki na dogon lokaci.