A tarihin Duniya, ƙarni na 19 ya kasance lokaci na gagarumin sauye-sauye—lokacin da ƙasashen Turai suka shiga fafatawar neman iko, arziki, da faɗaɗa tasiri a Duniya.
Wannan lokaci ne da aka cika da manyan ayyuka na fasaha da gine-gine, kamar layukan Dogon Jirgin Ƙasa da suka haɗa Birane da Ƙasashe, domin sauya yanayin kasuwanci da hulɗar al’umma baki ɗaya.
Amma a cikin wannan ci gaba, akwai kuma wani ɓangare mai cike da haɗari—wato yunƙurin mallakar sabbin yankuna, musamman a Nahiyar Afirka. Wannan ne ya haifar da abin da aka sani da ‘Scramble for Africa,’ in da ƙasashen Turai suka raba Nahiyar Afirka kamar wata dukiya, ba tare da la’akari da al’ummomin da ke zaune a cikinta ba.
A wannan yanayi ne Faransa, wacce ta fito daga rushewar Daular Napoléon Bonaparte, ta fara neman hanyoyin dawo da martabarta da ƙarfin tattalin arzikinta. Bayan ta rasa yankuna da dama da tasirinta ya ragu, hankalinta ya karkata zuwa Afirka—musamman bayan ta mallaki Aljeriya a shekarar 1830.
Sai dai maimakon ta tsaya a bakin Teku kamar yadda wasu ƙasashe suka yi, Faransa ta ɗora idanuwanta kan wani wuri mai tsananin wahalar sha’ani—Hamadar Sahara. Wuri mai faɗi, tsauri, kuma mai cike da asirai, wanda yawancin Turawa ke guje masa saboda haɗarinsa.
Duk da haka, wasu sun ga wannan Hamada a matsayin wata babbar dama—dama ta kasuwanci, arziki, da kuma iko. A cikin wannan tunani ne aka samar da wani babban buri: Gina Layin Dogon Jirgin Ƙasa da zai ratsa Sahara, ya haɗa Arewacin Afirka da tsakiyar Nahiyar.
Wannan buri ya zama abin sha’awa ga masu wannan tunani—amma a zahiri, ya kasance shiri mai cike da haɗari wanda daga ƙarshe ya haifar da ɗaya daga cikin manyan bala’o’in da Mulkin Mallaka ya fuskanta a tarihin Afirka.
Faransa Bayan Rushewar Daular Napoléon
A farkon ƙarni na 19, Faransa ta kasance cikin rauni mai tsanani. Bayan faɗuwar Napoléon Bonaparte, ta rasa yawancin yankunan da ta mallaka, ciki har da wasu Tsibirai da ta miƙa wa Birtaniya. Har ila yau, an tilasta mata biyan Diyya mai yawa—kimanin Franc miliyan 700.
A wannan lokaci, tunanin Turawa game da Sahara ya fara samun tasiri daga masu bincike kamar Henri Duveyrier, wanda ya yi rubuce-rubuce kan Tuareg, ya kuma bayyana su a matsayin Mutane masu ladabi da zaman lafiya.
Wannan fahimta ta yi tasiri sosai wajen tsara tunanin Faransa game da Sahara, amma daga baya ta zama tushen kuskuren zato a aikace.
Shirin Shiga Cikin Sahara
Bayan mamayar Aljeriya a shekarar 1830, Faransa ta fara kallon cikin Sahara a matsayin wata hanya ta faɗaɗa iko da kasuwanci. Duk da wahalar Hamada, sun yi imanin cewa akwai arziki mai yawa a cikinta:
- Ma’adinan ƙarfe
- Gishiri
- Phosphate (yawanci ana samun sa a cikin Duwatsu ko Ƙasa a matsayin ma’adini)
- Har ma da yiwuwar Noma ta hanyar ban ruwa (Irrigation)
Sai dai, don cimma wannan buri, dole ne su sami hanyar da za ta haɗa waɗannan yankuna—wanda ya kai su ga ra’ayin gina Layin Dogon Jirgin Ƙasa.
Ra’ayin Layin Dogon Jirgin Ƙasa
A shekarun 1870s, Injiniyoyi kamar Alphonse Duponchel da Paul Soleillet, sun gabatar da ra’ayin.
Manufar ita ce:
- Haɗa Aljeriya da Sudan da sauran yankunan Afirka
- Faɗaɗa kasuwanci
- Ƙarfafa ikon Faransa a Nahiyar
Haka kuma, wannan zai taimakawa Faransa ta yi gogayya da sauran ƙasashen Turai wajen mallakar arzikin Afirka.
Ƙalubalen Tuareg
Babban ƙalubale shi ne mutanen Sahara, wato Tuareg, masu sarrafa hanyoyin kasuwanci da ƙwarewa a rayuwar Hamada.
- Suke sarrafa hanyoyin kasuwanci
- Suke da gogewa da ƙwarewa a rayuwar Hamada
- Kuma ba sa amincewa da ƙarfa-ƙarfan baƙi
Paul Flatters da Burinsa

Paul Flatters, ya kasance Soja kuma jami’in gudanarwa na Faransa, wanda ya shafe mafi yawan aikinsa na Soja a Aljeriya. Ya kasance mai ƙwazo da sha’awar kafa sunansa a matsayin wanda zai iya cika burin gina Layin Dogon Jirgin Ƙasa da zai ratsa Sahara.
Ya kasance mai tunani na musamman, wanda ba ya bin tsari ɗaya kawai, kuma ya na faɗin ra’ayinsa a sarari ga manyansa ba tare da ɓoyewa ba. Misali, ya taɓa ba da shawarar cewa Faransa ta amince da wani mataki na bautar da Mutane, domin hakan zai taimaka mata wajen shiga cikin Hamada cikin sauƙi.
Sai dai a wannan lokaci, Faransa ta ri ga ta haramta bautar da Mutane, duk da cewa har yanzu ana yin irin wannan aiki a wasu sassan Nahiyar Afirka da wani salo na matsin tattalin arziki.
A wannan lokaci ne Paul Flatters ya fito da ƙudirin jagorantar wannan aiki.
Ya yi ƙoƙarin ya fahimci Tuareg, ya koyi harshen Larabci, amma ya yi kuskure wajen ganin zai iya shawo kansu cikin sauƙi.
Haka nan, ya kasance mai buri sosai—wadda ya sa ya raina haɗarin da ke gabansa.

Balaguron 1880-1881
A da can, wani mai bincike ɗan ƙasar Faransa mai suna Henri Duveyrier, wanda tun ya na saurayi ya yi wata muhimmiyar tafiya zuwa Arewacin Hamadar Sahara wadda ta sauya rayuwarsa gaba ɗaya, ya rubuta cikakkun bayanai game da mutanen Tuareg.
Wannan bincike nasa ne ya buɗe masa ƙofa, har ya zama mashawarci ga Gwamnatin Faransa kan al’amuran da suka shafi Afirka. Ya riƙa bayar da shawarar cewa, a gina dangantaka ta zaman lafiya tsakanin Faransa da Afirka, maimakon tsarin Iko da Mulkin Mallaka.
Duveyrier, ya goyi bayan ra’ayin gina Layin Dogon Jirgin Ƙasan, kuma ya amince a fara aikin binciken fara gudanar da aikin.
Bai yi tsammanin cewa Tuareg za su cutar da tawagar ba. A cikin rubuce-rubucensa, ya bayyana su a matsayin Mutane masu wayewa, masu haƙuri, kuma masu nisantar al’amuran Turawa.
An raba tawagar binciken zuwa sassa uku domin duba wurare uku da za su iya zama matattarar fara gina Layin Dogon Jirgin Ƙasa, wato:
- Oran
- Algiers
- Constantine
A kowane ɗaya daga cikin waɗannan wurare, masu binciken dole ne su:
- Nemo hanyoyin samun ruwa
- Wuce yankunan da Tuareg ke iko da su
- Auna da nazarin ƙasar, da kuma tsara hanyoyin da layin Dogon Jirgin Ƙasa zai bi
A ranar huɗu ga Disamba, 1880, tawagar Flatters ta tashi daga Ouargla zuwa cikin Sahara.
Tafiyar ta kasance lafiya yadda ya kamata, har sai da suka isa Bir al-Garama, wata Rijiya a Kudancin Aljeriya wanda mutanen Tuareg ke lura da ita, a nan ne Tuareg suka farmake su:
- Aka kashe Flatters
- Aka tarwatsa tawagar
- Aka ƙwace Raƙuma da kayayyakinsu
Mummunan Ƙarshe
Bayan harin, waɗanda suka tsira sun shiga cikin matsananciyar yunwa da ƙishirwa.
A watan Fabrairu na shekarar 1881, yayin da yunwa da ƙishirwa suka tsananta a kan mutanen tawagar, wasu daga cikin Tuareg suka nuna kamar tausayi gare su, in da suka ba su Madara, Nama, da dabino—amma kan farashi mai tsananin tsada.
Mutanen tawagar suka biya kuɗin, suka kuma ci saboda tsananin yunwa. Sai dai ba da daɗewa ba suka fara jin mummunan murɗawar ciki mai tsanani.
Ashe kuwa, mutanen Tuareg sun ɓoye sun haɗa abincin da guba daga wata tsiro ta cikin Hamada.
Daga baya:
- An ba su Abinci mai guba
- Sun kamu da Amai da Gudawa
- Wasu da dama sun Mutu daga cikinsu
Waɗanda suka rage:
- Sun fara kashe junansu
- Yunwa ta kai su ga cin naman ƴan’uwansu
A ƙarshe, kaɗan daga cikinsu suka tsira suka koma Ouargla a watan Afrilun 1881.
Wane ne ke da Laifi?
Masana tarihi su na ganin laifin ya fi kan Paul Flatters saboda:
- Ya raina wahalar Sahara
- Ya kasa fahimtar Tuareg
- Ya dogara da buri maimakon shiri mai ƙarfi
- Ya wuce gona da iri wajen yarda da kansa
Masani John Strachan daga Jami’ar Lancaster ya bayyana shi a matsayin Mutum mai buri amma bai dace da shugabanci ba.
Sai dai kuma, akwai laifin tsarin fahimta gaba ɗaya, wanda ya samo asali daga Taswirar Tuareg da aka zana tun farko.
Tsarin Tunani da Ilimi

Hoton Taswirar Tuareg da Henri Duveyrier ya zana da kuma bayanan da ya rubuta, ya sa aka yi kuskuren fahimta.
Wannan hoton da rubutun da ya yi, ya sa aka ɗauka cewa Tuareg:
- Masu sauƙin hulɗa ne
- Ba za su yi tirjiya mai tsanani ba
Alhali gaskiya ta bambanta da haka.
Makomar Henri Duveyrier Bayan Balaguron

Henri Duveyrier, ya yi tasiri sosai a fahimtar Faransa game da Tuareg. Amma bayan gazawar balaguron, an zarge shi da cewa, ya nuna Tuareg a matsayin “Medieval Paladins,”
- Jaruman Zamani masu ɗa’a, mutunci da girmamawa
- Masu sauƙin sha’ani da tsayayyen ra’ayi kamar mutanen da
Wanda daga baya suka ce bai dace da gaskiyar halayensu ba.
Wannan zargi ya jefa shi cikin baƙin ciki mai tsanani, musamman bayan rasuwar masoyiyarsa, har daga ƙarshe ta kai ga ya kashe kansa a shekarar 1892.
Tasirin Bala’in
A cewar Douglas Porch, marubucin littafin ‘The Conquest of the Sahara,’ wannan bala’i ya sa Faransa ta janye daga wannan buri bayan ɗan lokaci, duk da fusata da ta yi, da kuma kiran ramuwar gayya.
Ƙarshen Alewa Ƙasa
Layin Dogon Jirgin Ƙasa na Sahara bai taɓa kammaluwa ba.
An sake yunƙurin farfaɗo da shi a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, amma:
- Ma’aikata sun kamu da cututtuka
- Kuɗi ya ƙare
- Ayyuka suka tsaya
A yau, abin da ya rage kawai shi ne, wasu ragowar ɓaraguzan layi da suka nutse cikin yashin Sahara—shaida ta wani mafarki da bai cika ba.
Darasi daga Tarihin
Wannan lamari ya na nuna:
- Iyakokin ƙarfin Ɗan’Adam a kan wata al’umma
- Muhimmancin fahimtar al’adu kafin shiga wata al’umma
- Haɗarin girman kai da rashin cikakken shiri
Da kuma yadda kuskuren fahimta na iya haifar da bala’i mai girma.
MADOGARA
- Porch, Douglas. The Conquest of the Sahara.
- Strachan, John. Nazarin Balaguron Mulkin Mallaka na Faransa a Sahara (Lancaster University).
- Duveyrier, Henri. Rubuce-rubuce kan Sahara da Tuareg (Exploration du Sahara da sauran bayanai).
- Tarihin Mulkin Mallaka na Faransa a Aljeriya (1830–1881).
- Rahotannin “Flatters Expedition” na tarihin Soja na Faransa.
- Nazarin “Scramble for Africa” a tarihin Turai da Afirka.


Ivy3686
05/05/2026https://shorturl.fm/UOLCw
Israel984
05/05/2026https://shorturl.fm/V2Cwg
Brady3539
05/05/2026https://shorturl.fm/EdIbm
Paul1716
05/05/2026https://shorturl.fm/0Y2ak
Doug190
05/05/2026https://shorturl.fm/7rA7m
Martin1618
05/05/2026https://shorturl.fm/xj0YF
Hank699
05/05/2026https://shorturl.fm/5PmBg
Carson3494
05/05/2026https://shorturl.fm/tlG7k
Adam598
05/05/2026https://shorturl.fm/mUCLq
Harper1944
05/05/2026https://shorturl.fm/mRid7