Najeriya ta kasance Ƙasa ta Bakwai a Duniya wajen kyautatawa da taimakon baƙi, yayin da kuma ta zo ta 105 a ma’aunin farin ciki da walwala, kamar yadda rahoton Farin Cikin Duniya na shekarar 2025, na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya nuna.
Rahoton na 2025, wanda Cibiyar Bincike ta Jin Daɗin Rayuwa ta Jami’ar Oxford ta haɗa tare da Gallup da kuma UN Sustainable Development Solutions Network, ya tantance ƙasashe 147 bisa yadda jama’a ke bayyana jin daɗin rayuwarsu, tare da halayen taimakon jama’a kamar; taimakawa wasu, aikin sa-kai, da bayar da gudunmowa.
Duk da cewa Najeriya ta samu matsayi na bakwai wajen kyautatawa baƙi, matsayinta a ma’aunin farin ciki da walwalar jama’a ya faɗi zuwa na 105, abin da ke nuna ƙalubale irin su; rashin samun ingantacciyar rayuwa, da kuma ƙarancin amincewa da hukumomin Gwamnati.
Rahoton ya nuna akwai babban giɓi na aminci da yarda a Najeriya, in da Mutane suka fi yarda da baƙi fiye ƴanƙasa da kuma Gwamnati.
A yayin tattara bayanai a lokacin haɗa rahoton, an yi tambayar cewa, “Shin wa zai mayar da walat ɗin kuɗi idan ya tsinta?” Najeriya ta kasance ta 33 idan baƙo ne ya tsinta, ta 71 idan maƙwabci ne, sannan ta 126 idan Ƴansanda ne suka tsinta.
Rahoton ya ce:
“A wuraren da tsarin hukumomi yake da rauni, taimaka wa baƙi kan zama hanya mafi sauƙi kuma mafi tasiri ta nuna alheri.”
Rahoton ya bayyana cewa, irin wannan yanayi ya na faruwa a wasu ƙasashe masu raunin tsarin hukumomi kamar: Jamaica, Laberiya, Trinidad & Tobago, Kenya, Saliyo, Senegal, Venezuela, Ukraine da Zambiya.
Bugu da ƙari, Najeriya ta zo ta 45 a Duniya wajen bayar da gudunmowar jin ƙai, abin da ke ƙara nuna yadda al’ummar ƙasar ke da ɗabi’ar taimakon juna duk da matsalolin da ƙasar ke fuskanta na tattalin arziki.


Jeff2777
07/05/2026https://shorturl.fm/NGu0j
Simon96
07/05/2026https://shorturl.fm/EOGFl
Eliza4816
07/05/2026https://shorturl.fm/9f03V
Emmett1597
07/05/2026https://shorturl.fm/Q0PCU
Cedric4729
07/05/2026https://shorturl.fm/GmxF5
Mallory4540
07/05/2026https://shorturl.fm/Uu18z
Kiley2953
07/05/2026https://shorturl.fm/ncvrI
Allison135
07/05/2026https://shorturl.fm/9nKU1
London3792
07/05/2026https://shorturl.fm/KcUWE
Blair3808
07/05/2026https://shorturl.fm/W7nGc
Julius3130
07/05/2026https://shorturl.fm/ycr4J
Lawrence1034
07/05/2026https://shorturl.fm/FUKC1
Kim2705
07/05/2026https://shorturl.fm/PhJy8
Aylin625
07/05/2026https://shorturl.fm/yPFZb
Donovan1616
07/05/2026https://shorturl.fm/ddrrH
Terry3503
07/05/2026https://shorturl.fm/qjX5I
Destiny1069
07/05/2026https://shorturl.fm/zf7vQ