Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Masarautu

Tarihin Daular Kabawan Kanta: Daga Surame Zuwa Argungu

Gabatarwa

Daular Kabi na daga cikin manyan daulolin da suka yi fice a tarihin Yammacin Sudan da kuma ƙasar Hausa kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka. Daular ta shahara saboda ƙarfin mayaƙanta, faɗin yankunan da ta mallaka, da kuma rawar da ta taka a harkokin siyasa, kasuwanci da yaƙe-yaƙe a tsakanin ƙarni na 15 zuwa na 19.

Tarihin Daular Kabi ya haɗu da tarihin jarumin Sarki Muhammadu Kanta Kotal, wanda ya kafa daular tare da gina ta zuwa ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu ƙarfi a wannan yanki.

Duk da cewa Daular ta fuskanci ƙalubale da dama a tsawon rayuwarta, har ta kai ga rugujewar tsohuwar cibiyarta, al’adun Kabawa da sarautarsu sun tsira, kuma daga bisani suka sake kafa sabon Birni a Argungu wanda ya ci gaba da zama cibiyar Kabawa har zuwa yau.

               Asalin Kabawa

Akwai ruwayoyi daban-daban game da asalin Kabawa. Wasu ruwayoyin gargajiya su na cewa, kakannin Kabawa sun samo asali ne daga Larabawa, kuma su na da alaƙa da masu kula da Ka’abah a Makkah. A cewar wannan ruwaya, daga kalmar “Ka’abah” ne aka samo sunan “Kabawa”.

Sai dai masana tarihi ba su da hujjojin da suka tabbatar da wannan labari gaba ɗaya. Saboda haka, ana kallon sa a matsayin wata ruwayar gargajiya da al’ummar Kabawa suka gada daga kakanninsu.

Abin da ya fi samun karɓuwa a tarihin da aka rubuta shi ne cewa, Kabawa sun kasance wata al’umma mai ƙarfi a yankin Yammacin Sudan, kuma sun haɗu da sauran al’ummomin Hausawa, Songhai, Zabarmawa da Borgawa ta hanyar kasuwanci, auratayya da hulɗar Siyasa.

Muhammadu Kanta Kotal da Kafuwar Daular Kabi

Muhammadu Kanta Kotal shi ne wanda aka fi dangantawa da kafuwar Daular Kabi. Ya rayu a ƙarshen ƙarni na 15 da farkon ƙarni na 16.

A cewar wasu ruwayoyi, mahaifiyarsa ta na da alaƙa da Gidan Sarautar Katsina. Haka kuma, wasu labarai su na cewa, Kanta ya taso ne a Katsina kafin daga bisani ya bar garin saboda saɓanin da ya shafi Sarauta.

Bayan ya bar Katsina tare da mabiyansa, ya zauna a Surame, wani tsohon Gari da ke yankin da yanzu yake cikin Jihar Sakkwato. A nan ne ya fara tara mayaƙa da magoya baya, tare da gina tubalin daular da daga baya ta zama Daular Kabi.

Kanta ya shahara da jajircewa, dabara da kuma iya jagoranci. Waɗannan halaye ne suka taimaka masa wajen kafa Daula mai ƙarfi a lokacin da yankin ke fama da gasa tsakanin manyan Ƙasashe da Dauloli.

Birnin Surame: Tsohon Babban Birnin Kabi

Surame shi ne babban birnin farko na Daular Kabi.

Birnin ya kasance ɗaya daga cikin manyan biranen da aka gina a Yammacin Sudan a lokacin. An kewaye shi da katafariyar Ganuwa mai tsawo da Ƙofofi da dama domin kare shi daga hare-haren maƙiya.

A yau, ragowar Ganuwar Surame da sauran gine-ginen birnin har yanzu su na nan, kuma su na daga cikin muhimman wuraren tarihi a Najeriya. Kufen wannan birni su na nuna irin ci gaban da Daular Kabi ta samu tun kafin zuwan Turawa.

Dangantakar Kabi da Daular Songhai

A lokacin da Kanta ke kafa daularsa, Daular Songhai ta na daga cikin manyan Daulolin Afirka. A ƙarƙashin jagorancin Sarki Askiya Muhammad, Songhai ta faɗaɗa ikonta zuwa yankuna masu yawa.

Da farko, an samu saɓani tsakanin Kabi da Songhai. Bayan wasu faɗace-faɗace, an cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin Kanta da Askiya Muhammad.

Wannan sulhu ya haifar da haɗin guiwa a tsakanin daulolin biyu, in da suka yi yaƙe-yaƙe tare a wasu yankuna. Amma daga baya dangantakar ta lalace sakamakon rikice-rikicen siyasa da gwagwarmayar neman cikakken ƴancin kai.

Kanta ya yi ƙoƙarin tabbatar da cewa, Daular Kabi ba ta ƙarƙashin ikon Songhai ba ce. Wannan ya kai ga yaƙe-yaƙe masu tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.

Duk da ƙarfin Songhai, mayaƙan Kanta sun yi nasarar kare ƙasarsu, lamarin da ya ƙara ɗaukaka sunan Daular Kabi a faɗin Yammacin Sudan.

            Faɗaɗuwar Daular Kabi

Bayan samun ƙarfi, Muhammadu Kanta ya fara faɗaɗa yankunan daularsa.

Daga cikin yankunan da tasirin Daular Kabi ya kai akwai:

  • Gobir
  • Zamfara
  • Yauri
  • Borgu
  • Gurma
  • Agades
  • Wasu sassa na Nupe

Haka kuma, mayaƙan Kabi sun yi yaƙe-yaƙe da wasu manyan ƙasashe irin su Kwararrafa da wasu ƙananan Masarautu.

Faɗaɗuwar daular ba kawai ta kawo ƙarfin Soja ba ce, har ma ta bunƙasa Kasuwanci, Noma da harkokin Sufuri tsakanin yankuna daban-daban, da kuma ƙarfafa matsayin Kabi a siyasar yankin.

Tsarin Mulki da Ƙarfin Soja

Daular Kabi ta shahara wajen tsara rundunonin mayaƙa masu ƙarfi.

Sarauta ita ce cibiyar mulki, yayin da Sarakuna da Hakimai ke kula da yankuna daban-daban. Mayaƙan daular su na amfani da Dawaki da Makamai na gargajiya wajen kare Iyakoki da kuma gudanar da yaƙe-yaƙe.

Ƙarfin mayaƙan Kabi ya sanya daular ta zama abin tsoro ga maƙwabtanta na tsawon lokaci.

     Jerin Sarakunan Daular Kabi

Tun daga kafuwar Daular Kabi a hannun Muhammadu Kanta Kotal, sarakuna da dama sun gaji gadon mulki. Daga cikin waɗanda aka fi sani akwai:

  • Muhammadu Kanta Kotal (1516–1561)
  • Ahmadu I (1561–1596)
  • Dawuda (1596–1619)
  • Ibrahimu I (1619–1621)
  • Suleimanu I (1621–1636)
  • Muhammadu (1636–1649)
  • Maliki ɗan Ibrahimu (1649–1662)
  • Umaru Ciwa (1662–1674)
  • Muhammadu Kaye (1674–1676)
  • Ibrahimu II (1676–1684)
  • Muhammadu na Sifawa (1684–1686)
  • Ahmadu ɗan Amaru (1686–1696)
  • Tomo (1696–1700)
  • Muhammadu ɗan Giwa (1700–1717)
  • Samaila (1717–1750)
  • Muhammadu ɗan Tagande (1750–1754)
  • Abdullahi Toga (1754–1775)
  • Suleimanu II (1775–1803)
  • Abubakar Ukar (1803)
  • Muhammadu Hodi (1803–1826)

Waɗannan Sarakuna ne suka jagoranci daular tun daga zamanin Surame har zuwa ƙarshen tsohuwar Daular Kabi.

         Mafarin Raunanar Daular

Bayan rasuwar Muhammadu Kanta, magadansa sun ci gaba da mulki, amma ba su kai shi ƙwarewa da ƙarfin jagoranci ba.

A hankali rikice-rikicen cikin gida suka fara bayyana. Haka kuma ƙananan yankunan da ke ƙarƙashin Kabi suka fara ƙoƙarin ƙwace ƴancinsu.

A lokaci guda, hare-haren maƙwabta da sauye-sauyen Siyasa a Yammacin Sudan suka ƙara raunana daular.

Sauya Babban Birni Zuwa Birnin Kebbi

Fadar Masarautar Kabi

A lokacin Sarki Tomo, matsalolin tsaro da yaƙe-yaƙe suka sa aka ɗauke babban Birnin Daular daga Surame zuwa wani sabon wuri.

Daga baya aka kafa Birnin Kebbi, wanda ya zama sabon Babban Birnin Daular. Wannan mataki ya taimaka wajen ci gaba da rayuwar Daular duk da ƙalubalen da take fuskanta.

Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da Kabi

A farkon ƙarni na 19, Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya sauya taswirar siyasar Arewacin Najeriya.

Sojojin Jihadi ƙarƙashin jagorancin Shehu Abdullahi Ɗanfodiyo sun fafata da Daular Kabi. Bayan jerin yaƙe-yaƙe, aka ci Daular Kabi da yaƙi a shekarar 1805.

Wannan nasara ta kawo ƙarshen tsohuwar Daular Kabi a matsayin Babbar Ƙasa mai cin gashin kanta.

Kafuwar Argungu da Sake Farfaɗowar Kabawa

Duk da faduwar tsohuwar Daular Kabi, Kabawa ba su shuɗe ba.

A ƙarƙashin Sarki Muhammadu Hodi, Kabawa suka sake tattaruwa tare da kafa sabon Birni mai suna Argungu a shekarar 1827.

Argungu ta zama sabon babban birnin Kabawa, kuma daga nan aka sake gina tsarin sarauta da al’adunsu.

Tun daga wannan lokaci, Argungu ta ci gaba da zama cibiyar tarihin Kabawa da masarautarsu.

          Jerin Sarakunan Argungu

Tun bayan kafuwar Argungu, Sarakuna da dama sun mulki masarautar:

  • Samaila Karari (1827–1831)
  • Yakubu Nabame (1831–1854)
  • Yusufu Mainasara (1854–1859)
  • Muhammadu Ba’are (1859–1860)
  • Abdullahi Toga (1860–1883)
  • Samaila II (1883–1915)
  • Suleimana (1915–1920)
  • Muhammadu Sama (1920–1934)
  • Muhammadu Sani (1934–1942)
  • Samaila III (1942–1953)
  • Muhammadu Shefe (1953–1959)
  • Muhammadu Mera (1959–1996)
  • Samaila Muhammadu Mera (1996– 2024)
  • Muhammadu Samaila Mera 2024–zuwa yau).

Sarkin Kabin Argungu na Yanzu

Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Muhammadu Samaila Mera.

Bayan rasuwar Samaila Muhammadu Mera a shekarar 2024, an naɗa Muhammadu Sama’ila Mera a matsayin Sarkin Kabin Argungu na 31, wanda ke ci gaba da jagorantar Masarautar a yau.

Gidan Nabame (Kanta Museum)

Daga cikin manyan wuraren Tarihi da suka rage a yau domin tunawa da tarihin Daular Kabawa akwai Gidan Nabame, wanda aka fi sani da Kanta Museum. Wannan Gida na daga cikin fitattun Gidajen Adana Kayan Tarihi a Najeriya, kuma ya na cikin Garin Argungu na Jihar Kebbi, kusa da tsohuwar kasuwar garin.

An gina wannan katafaren gini a shekarar 1831, kuma an sanya masa suna ne domin tunawa da Muhammadu Kanta Kotal, wanda ya kafa Daular Kabi a farkon ƙarni na 16.

Kanta ya kasance ɗaya daga cikin manyan sarakunan da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa da faɗaɗa Daular Kabi, har ta zama ɗaya daga cikin manyan Daulolin Yammacin Sudan.

Tsohon Sarkin Kabi Yakubu Nabame ne ya gina wannan Fada, wadda ta kasance cibiyar mulkin Sarakunan Kabi na tsawon lokaci.

Fadar ta ci gaba da zama mazaunin sarakuna har zuwa shekarar 1942, lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka gina sabuwar Fadar Sarauta a zamanin Sarkin Kabi Muhammadu Sani.

Bayan an daina amfani da ita a matsayin Fadar Sarauta, an mayar da ginin Gidan Kayan Tarihi, kuma aka buɗe shi ga jama’a a ranar 1 ga Yuli, 1958. Tun daga wannan lokaci, Gidan Tarihin ya zama muhimmiyar cibiyar adana tarihin Kabawa, al’adunsu, yaƙe-yaƙensu, da kuma rayuwar sarakunansu.

A cikin Gidan Tarihin akwai tarin kayayyakin tarihi da suka haɗa da:

  • Makaman yaƙi na gargajiya
  • Takubba, Mashi da Garkuwoyi
  • Kayan Sarauta
  • Kayan Noma da Farauta
  • Kayan ado na gargajiya
  • Tsofaffin kayayyakin amfanin Gida na gargajiya
  • Kayayyakin da aka samu daga yaƙe-yaƙen da Kabawa suka yi da sauran Masarautu.

Waɗannan kayayyaki su na taimakawa masu ziyara su fahimci tarihin Daular Kabi da rawar da ta taka a tarihin Arewacin Najeriya.

Ƙaburburan Sarakunan Kabawa

Wani muhimmin abu da ya bambanta Gidan Nabame da sauran Gidajen Tarihi shi ne; kasancewarsa wurin da ake binne Sarakunan Kabawa bayan rasuwarsu.

A al’adar Masarautar Argungu, idan Sarkin Kabi ya rasu, ana mayar da gawarsa Argungu domin a binne ta a cikin harabar Gidan Nabame, ko da kuwa ya rasu a wani Gari ko wata Ƙasa mai nisa. Wannan al’ada ta daɗe ta na gudana tun ƙarni na 19, kuma har yanzu ana ci gaba da kiyaye ta.

Saboda haka, Gidan Nabame ba kawai gidan kayan tarihi ba ne, har ila yau Maƙabarta ce ta Sarakunan Kabawa. Ƙaburburan da ke cikinsa su na wakiltar sarakunan da suka jagoranci Kabawa bayan kafuwar Argungu, kuma su na zama wata muhimmiyar shaida ta ci gaba da wanzuwar Masarautar.

Masu ziyara daga sassa daban-daban na Najeriya da ma ƙasashen waje kan ziyarci wurin domin ganin waɗannan ƙaburbura tare da nazarin tarihin sarakunan da suka mulki Argungu tsawon shekaru.

Muhimmancin Gidan Nabame ga Tarihin Kabawa

Gidan Nabame ya haɗa abubuwa uku masu muhimmanci a tarihin Kabawa:

  • Tsohuwar Fadar Sarakunan Kabi
  • Gidan Adana Kayan Tarihin Kabawa
  • Maƙabartar Sarakunan Kabawa

Saboda haka, duk wanda yake son fahimtar tarihin Daular Kabi da Masarautar Argungu, Gidan Nabame na daga cikin wuraren da ya kamata ya ziyarta. Ginin ya na wakiltar kusan ƙarni biyu na tarihin Sarauta, kuma ya na ci gaba da zama ɗaya daga cikin muhimman wuraren tarihin Arewacin Najeriya da suka rage har zuwa yau.

                 Kabawa a Yau

A yau, Masarautar Argungu ta na daga cikin manyan Masarautun Jihar Kebbi.

Yankunan da ke ƙarƙashinta sun haɗa da:

  • Argungu
  • Augie
  • Arewa
  • Dandi

Al’ummar yankin su na magana da Harshen Hausa, tare da kasancewar Zabarmawa, Fulani da wasu ƙabilu da dama da suke zaune a yankin.

Har ila yau, Kabawa sun ci gaba da riƙe al’adunsu, musamman ta hanyar bukukuwa, sarauta da kuma kiyaye wuraren tarihinsu.

Akwai ruwayoyi daban-daban game da asalin Kabawa. Wasu ruwayoyin gargajiya su na danganta asalinsu da Larabawa da masu kula da Ka’abah, sai dai masana tarihi ba su samu hujjojin da suka tabbatar da wannan labari gaba ɗaya ba.

Bikin Kamun Kifi na Argungu

Asalin Bikin

Bikin Kamun Kifi na Argungu na daga cikin tsofaffin bukukuwan gargajiya a Najeriya.

Asalinsa ya na da alaƙa da zaman lafiya da aka samu tsakanin Masarautar Argungu da Khalifancin Sakkwato bayan shekaru na rikice-rikice da yaƙe-yaƙen da suka biyo bayan Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo a farkon ƙarni na 19.

Bayan da zaman lafiya ya samu tsakanin ɓangarorin biyu, shugabannin yankunan suka fara shirya bukukuwa da wasanni domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin al’ummominsu. Daga cikin waɗannan bukukuwa ne aka samu Bikin Kamun Kifi na Argungu wanda daga baya ya zama sananne a Duniya.

An fara gudanar da bikin a tsarinsa na zamani a shekarar 1934, lokacin da Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama ya karɓi baƙuncin Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu’azu. Wannan ziyara ta ƙara ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Argungu da Sakkwato, kuma daga nan ne bikin ya samu ƙarin shahara.

Kamun Kifi: Babban Jigon Bikin

Babban abin da ya fi jan hankali a bikin shi ne Gasar Kamun Kifi da ake yi a Kogin Matan Fada.

A ranar bikin, dubban Masunta kan shiga Ruwa lokaci guda ɗauke da kayan kamun Kifi na gargajiya. Kowane mahalarta ya na ƙoƙarin kamo mafi girman Kifi cikin ƙayyadadden lokaci.

A da, wanda ya kamo mafi girman Kifi kan samu kyaututtuka kamar Kuɗi, Shanu, Raƙuma, ko wasu manyan kyaututtuka daga Sarakuna, da Gwamnati, Attajirai, da Kamfanoni. A yau kuwa, ana ba da manyan kyaututtuka da suka haɗa da Motoci, Kuɗaɗe da sauran lambobin yabo.

Wasannin Gargajiya na Bikin

Duk da cewa, kamun Kifi shi ne ya fi shahara, bikin ya ƙunshi tarin wasanni da al’adun gargajiya da suka kasance wani muhimmin ɓangare na rayuwar Kabawa da sauran al’ummomin yankin.

                     Kokawa

Kokawa na daga cikin fitattun wasannin da ake gudanarwa a lokacin bikin. Jarumai daga yankuna daban-daban kan fafata domin nuna ƙarfi, jarumta da fasahar Dambe irin ta gargajiya.

                     Harbin Baka

Harbin Baka wata tsohuwar sana’a ce da ta samo asali daga horon mayaƙa. A lokacin bikin, ƙwararrun Maharba kan nuna ƙwarewarsu wajen harbin abin da aka sa gaba.

        Tseren Kwale-Kwale

Masunta da matuƙan ruwa kan fafata a tseren Kwale-Kwale, in da suke nuna bajintarsu wajen sarrafa Kwale-Kwale cikin sauri a Ruwa.

              Wasannin Ruwa

Akwai wasu wasanni daban-daban da ake gudanarwa a Ruwa, waɗanda ke nuna ƙwarewar al’ummar yankin wajen mu’amala da koguna da harkokin kamun Kifi.

                Hawan Dawaki

Kamar sauran Masarautun Hausawa, Argungu ta na da tarihin Hawan Doki. A lokacin bikin, Mahaya daga Masarautu daban-daban kan fito cikin kayan alfarma domin nuna martabar sarauta da al’adun gargajiya.

           Rawar Gargajiya da Kiɗa

Ƙungiyoyin Makaɗa da Mawaƙa daga yankuna daban-daban kan halarci bikin domin gabatar da Waƙoƙi, Kirari da Raye-rayen gargajiya da ke nuna tarihin Kabawa da al’adunsu.

Muhimmancin Bikin ga Al’adu

Bikin Kamun Kifi na Argungu ya taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye al’adun gargajiya da suka gada tun ƙarni da dama.

Bikin ya ba da dama ga Matasa su san tarihin kakanninsu, su koyi wasannin gargajiya, sana’o’i da al’adun da suka kasance ginshiƙin rayuwar al’umma kafin zuwan zamani.

Har ila yau, bikin ya na taimakawa wajen haɗa al’ummomi daban-daban ba tare da la’akari da bambancin Ƙabila, Harshe ko matsayi ba.

Muhimmancin Bikin ga Tattalin Arziki

Bikin Kamun Kifi na Argungu na daga cikin manyan abubuwan da ke bunƙasa tattalin arzikin Jihar Kebbi.

A lokacin bikin, dubban Mutane daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje kan ziyarci Argungu. Wannan na ƙara yawan ciniki a kasuwanni, Otal-otal, Gidajen cin Abinci, harkokin sufuri da sana’o’in hannu.

Masu sana’o’i kan samu damar baje kolin kayayyakinsu, yayin da Manoma, Masunta da ƴan kasuwa ke samun sabbin kasuwanni da abokan hulɗa.

Saboda haka, bikin ya zama wata muhimmiyar hanya ta samar da ayyukan yi da kuma ƙara kuɗaɗen shiga ga al’ummar yankin.

         Matsayin Bikin a Duniya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Kebbi Umar Namadi da sauran baƙi yayin bikin.

Saboda muhimmancinsa a fannin al’adu da tarihi, Bikin Kamun Kifi na Argungu ya samu karɓuwa a matakin Ƙasa da Ƙasa. Ya zama ɗaya daga cikin fitattun bukukuwan al’adu da Yawon buɗe ido a Afirka, kuma ya taimaka wajen bayyana tarihin Kabawa ga Duniya baki ɗaya.

A shekarar 2016, Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNESCO, ta sanya Bikin Kamun Kifi na Argungu cikin jerin muhimman al’adun gargajiya da ya kamata a kiyaye domin amfanin al’ummomi masu zuwa. Wannan ya ƙara tabbatar da matsayin bikin a matsayin ɗaya daga cikin manyan al’adun gargajiya mafi shahara a Afirka.

                     Kammalawa

Daular Kabawan Kanta na daga cikin manyan daulolin da suka taka muhimmiyar rawa a tarihin Yammacin Sudan da ƙasar Hausa. Tun daga kafuwarta a Surame ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Kanta Kotal, zuwa sake farfaɗowarta a Argungu bayan Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, tarihin Kabawa ya kasance cike da jarumta, gwagwarmaya da ƙoƙarin kare martaba da ƴancin ƙasarsu.

Ko da yake tsohuwar Daular Kabi ta rushe, gadonta bai gushe ba. Har yau, Argungu, Gidan Nabame, ragowar Ganuwar Surame da Masarautar Kabawa su na ci gaba da zama shaidu na ɗaya daga cikin mafi girman daulolin da suka taɓa wanzuwa a tarihin Arewacin Najeriya.

                     MADOGARA

  1. britannica.com⁠. (Bayanai kan tarihin Argungu, Surame da Bikin Kamun Kifi).
  2. whc.unesco.org⁠. (Bayanai kan tsohon birnin Surame, katangunsa da muhimmancinsa a tarihin Daular Kabi).
  3. ich.unesco.org⁠. (Bayanai kan tarihin bikin, wasanninsa da muhimmancinsa wajen zaman lafiya da gadon al’adu).
  4. en.wikipedia.org⁠. (Bayanai kan tarihin ginin, kayan tarihin da ke cikinsa da kafuwarsa).
  5. nigeriagalleria.com⁠. (Ƙarin bayani kan Gidan Tarihin da Maƙabartar Sarakunan Kabawa).
  6. Palmer, H. R. Sudanese Memoirs. Lagos: Government Printer.
  7. Smith, Abdullahi. The Early States of the Central Sudan.
  8. M. G. Smith. Government in Zazzau 1800–1950.
  9. Murray Last. The Sokoto Caliphate.
  10. A. Mahadi. The Hausa Factor in West African History.
  11. Rubuce-rubucen Baka (Oral Traditions) da aka tattara daga tarihin Kabawa, Argungu da Surame.
Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

9 Comments

  1. Cornelius2509

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/PTc4l

  2. Diego2384

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/Oc7PL

  3. Serenity2623

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/aQg4Q

  4. Ryder3120

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/i2zZC

  5. Edmund1152

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/116kM

  6. Joseph292

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/Sg5dJ

  7. Alexa2852

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/qd4Tq

  8. Caden4184

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/eBCcT

  9. Leland3756

    10/06/2026

    https://shorturl.fm/9qEQw

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Masarautu

Tarihin Masarautar Pindiga

Daga: Faruk Tahir Maigari ✍️ Pindiga, babban Birnin Masarautar Pindiga ne da ke Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe, da
Masarautu

Tarihin Masarautar Katsina

Wannan rubutu da ake karantawa zai ba mu ƙarin haske game da wannan gari na Katsina. Katsina, babbar Masarauta ce,