Wace ce Nana Asma’u, ƴar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo
Daga: A’isha Aliyu Ja’afar Nana Asma’u ɗiya ce daga cikin ƴaƴa 23 na Shehu Usmanu Ɗanfodio, mujaddadin da ya jaddada addinin Musulunci a ƙarni na 17, a Arewacin Najeriya. Kasancewarta ƴan biyu – an haifi Asma’u tare da Hassan ɗinta a shekarar 1793, shekaru 11 kafin kafa Daular Usmaniyya kuma ta rasu a 1865 ta […]
