Daga: A’isha Aliyu Ja’afar
Nana Asma’u ɗiya ce daga cikin ƴaƴa 23 na Shehu Usmanu Ɗanfodio, mujaddadin da ya jaddada addinin Musulunci a ƙarni na 17, a Arewacin Najeriya.
Kasancewarta ƴan biyu – an haifi Asma’u tare da Hassan ɗinta a shekarar 1793, shekaru 11 kafin kafa Daular Usmaniyya kuma ta rasu a 1865 ta na da shekaru 72.
Duk da cewa Nana Asma’u, ba ita kaɗai ce ƴa mace ga Shehu Usmanu ba, amma sunanta ya fi shahara a kan na ƴan uwanta da suka haɗa da Aisha da Maryam da Fatima da kuma Hauwa’u.
Ana yi wa Nana laƙabi da sunaye kamar Asma’u Uwar Daje, ko Nana ko kuma Ma’u.
Iyalin Asma’u
A shekarar 1807 ne Nana Asma’u ta auri maigidanta Usman Giɗaɗo wanda ɗaya ne daga cikin manyan almajiran mahaifinta, Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da suka zauna da shi, kuma ɗaya daga cikin malaman da suka taimaka masa wajen gina Daular Usmaniyya.
Ƴaƴan Nana Asma’u guda biyar ne kuma dukkanninsu maza ne kamar yadda Jean Boyd da Beverly B. Mack suka rubuta:
- Abdulƙadir
- Ahmad
- Usman
- Abdullahi Bayero
- Muhammad Laima
Ilimantarwa

Nana Uwar Daji, ta shahara a fagen ilimantarwa musamman ga ƴan uwanta Mata, inda ta bai wa mahaifinta gagarumar gudunmowar sake wa Mata tunani a sabuwar Daular Musulunci dangane da yadda za su gudanar da ibadunsu na yau da kullum.
“Ta yi karatu mai zurfi a wurin mahaifinta, kuma masana tarihi sun ce ta na da gogewa a manyan harsuna uku – Larabci da Hausa da kuma Mashek (yaran Buzaye).
Hakazalika, ta ƙware a Fulantanci wanda kuma ta na rubutu da dukkan harsunan. Amma ta fi rubutu a Hausa da Larabci da kuma Fulatanci.” In ji dakta Abdullahi Hamisu Shehu, Malami a Tsangayar Tarihi da ke Jami’ar Bayero ta Kano.
Wani salo da Nana Asma’u ta yi amfani da shi wajen ilimantar da Mata a lokacin shi ne; ta hanyar Waƙe, kamar dai yadda mahaifinta ya yi wajen jan hankulan al’umma ba tare da tsaurarawa ba.
“Galibin rubutunta a Waƙe ta yi su, saboda Waƙa na da hikima da saurin isar da saƙo musamman idan ana rerawa.
Idan ana yi, Yara da Mata na haddacewa cikin ƙanƙanin lokaci, ba kamar rubutun zube ba,” in ji Dakta Abdullahi.
Makarantar Matan Aure na Farko
Kasancewar a zamanin babu ajujuwan koyarwa kamar na yau, amma tun a lokacin Nana Asma’u na da majalisai na koyarwa a cikin Gida, wanda za a iya cewa ita ta assasa abin da ake kira a yanzu, ‘Makarantar Matan Aure,’ saboda cikin almajiranta akwai Matan Aure da kuma ƴanmata.
Kuma hakan ne ya sa ta samu karɓuwa sannan abin da ta koyar ya yi naso.
“Abubuwan da take koyarwa sun yi naso, saboda har waɗanda ba sa zuwa makarantarta su na samun ilimin daga iyayensu ko ƴaƴa,” in ji Dakta Hamisu.
”A wannan lokacin babu kamarta wajen koyar da Mata, hakan ya ba ta kima da tasiri na musamman saboda gudunmowar da ta bayar wurin ilimantarwa.”
Idan aka cire Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, da ɗan’uwansa Sheikh Abdullahi bin Fodiyo da kuma ɗansa Muhammadu Bello, waɗanda za a ce sun bayar da gudunmowa kuma an tasirantu da su ta fuskar ilimantarwa a lokacinsu da lokacin baya, Nana Asma’u ce,” a cewar Dakta Hamisu.
Nana Asma’u ta yi tsawon rai inda ta rasu a lokacin ta na da shekaru 75 wanda ya ƙara mata tasiri sosai a zukatan mutane musamman Mata.
Saɓanin tunanin da ake yi wa Mata na gaza yin bautar Ubangiji kamar Maza, Nana Asma’u ta kasance Mace mai ƙoƙarin ibada da ta sallama rayuwarta wajen bautata wa Ubangiji tare da yi wa addinin Musulunci hidima.
”Tarihinta ya nuna ba ta da aiki sai ibada, da koyo da koyarwa, kuma saliha ce,” in ji Dakta Abdullahi.
Rubuce-rubucen Nana Asma’u
Ba a san iya yawan rubuce-rubucen Nana Asma’u ba kasancewar wasu sun ɓata, wasu sun lalace kafin a juya su zuwa tsarin rubutu na yanzu.
Sai dai an samu guda 66 da ke cikin gafakarta ta adana rubuce-rubucenta wadda take a gidanta.
Nana Asma’u ta rubuta su ne da harshen Larabci da Fulatanci da Hausa amma a salon Ajami.
Mafi yawancin rubuce-rubucen nata waɗanda a salon waƙe ne sun ƙunshi Tarihi da alhinin magabata da wa’azi da gargaɗi waɗanda su ne suka zama ginshiƙin da ya taimaka wajen riƙe Daular ta Usmaniyya.
Ga jerin wasu daga cikin rubuce-rubucen Nana Asma’u da ake yi laƙabi da Uwar Daji na muka naƙalto daga littafin “Collected Works of Nana Asma’u, Daughter of Usmanu Ɗanfodiyo (1793-1864) wanda Jean Boyd da Beverly B. Mack suka rubuta.
- Tabbat Hakika
- Tawassuli ga Mata Masu Albarka
- Waƙar Fadanci da Surorin Alkur’ani
- Waƙar Ahmada
- Waƙar Gewaye
- Godaben Gaskiya
- Muma Kan Nasara Yaƙi
- Alhinin Mutuwa
- Wa’azu
- Roƙon Ruwa
- Tsorace-Tsoracen Tsayin Al-Kiyama
- Dalilin Samuwar Allah
- Labaran Shehu
- Alhinin Mutuwar Modibbo Ɗan Ali
- Begore (Yabon Allah)
Masana na ganin cewa, waƙen da Nana Asma’u ta yi su ne suka zama ɗan-ba na ƙarfafa wa matan Daular Usmaniyya, watau; matan Arewacin Najeriya a yau ɗin nan guiwar yin Waƙe.
Nazari kan rayuwarta da Ayyukanta

Dakta Abdullahi Hamisu ya ce, Malaman Tarihi da dama daga wurare daban-daban sun yi bincike tare da nazari kan ayyukanta da abubuwan da ta faɗi kamar; darussan ibada, da na zamantakewa, da yadda za a kyautata rayuwa mai kyau, kusan duk abin da ya shafi addinin Musulunci ta yi rubutu a kai.
”Wannan ya sa aka yi ayyuka da yawa kan rubutunta na Larabci da Fulatanci da kuma Hausa, musamman fasalin rubutunta da saƙonnin da suke ƙunshe a ciki, inda aka taskace su aka kuma adana su,” in ji shi.
Ya kuma ce ko a shekarar 2019 tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya amince da kafa wata Jami’a ta koyar da aikin Likitanci da aka sanya wa sunan Nana Asma’u domin a ci gaba da tunawa da ita da ayyukanta da kuma gudunmowar da ta bai wa Musulmai a Arewacin Najeriya.

