Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'amuran Yau Da Kullum

Cocin Ingila ya Sake Jaddada Asusun Fam Miliyan 100 Kan Cinikin Bayi

Shugabar Cocin Ingila Dame Sarah Mullally, ta sake jaddada aniyar ci gaba da aiwatar da asusun Fam Miliyan 100 da aka tanada domin tallafa wa al’ummomin da har yanzu suke fama da illolin Cinikin Bayi na Tekun Atlantika, wanda ‘Church of England‘ ya amince ta na da hannu a tarihinsa.

Dame Sarah ta bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ta kai Cape Coast Castle a ƙasar Ghana, wurin da ake tsare dubban ƴan Afirka kafin a tilasta musu shiga Jiragen Ruwa zuwa nahiyar Amurka domin bautar da su.

Ta ce, ganin yanayin kurkukun da aka tsare bayin ya sake tuna mata da irin zalunci da cin zarafin da aka aikata, tare da jaddada cewa Cocin Ingila ya taka rawa a wannan tarihi.

A cewarta, tuba a koyarwar Addinin Kiristanci ba ta tsaya ga furuci kawai ba, dole ne ta kasance tare da ɗaukar matakan gyara. Saboda haka ne Cocin ke shirin aiwatar da shirye-shiryen da za su amfani al’ummomin da har yanzu suke ɗauke da raɗaɗin wannan tarihi.

A yayin ziyararta a Ghana, Dame Sarah Mullally ta bayyana goyon bayanta ga asusun diyya.

Wannan ne ziyararta ta farko zuwa nahiyar Afirka tun bayan da aka naɗa ta shugabar Cocin Ingila a wani bikin da aka gudanar a Canterbury Cathedral a watan Maris na wannan shekarar (2026).

A yayin ziyarar, batun adalci na gyara kura-kuran tarihi (Reparative Justice) ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ta mayar da hankali a kai.

Haka nan, a Cape Coast Castle, wanda ya shiga ƙarƙashin ikon Birtaniya a shekarun 1660, an zagaya da ita cikin kurkukun da ake tsare bayi kafin a fitar da su, tare da nuna mata abin da ake kira “Door of No Return” wadda ta kasance hanyar fitar da su, tare da tilasta wa bayin hawa jiragen ruwa domin kai su nahiyar Amurka, ba tare da fatan dawowa ƙasashensu ba.

Ta bayyana cewa, abin da ta gani ya girgiza zuciyarta, ya na kuma bayyana girman muguntar Cinikin Bayi na tekun Atlantika. Ta kuma nuna cewa kasancewar ɗakin ibada a saman kurkukun bayin wata shaida ce ta yadda Coci ya kasance cikin wannan tsarin a wancan lokaci.

Dame Sarah Mullally ta ce, abin da ta gani a yayin ziyararta zuwa Ghana ya matuƙar girgiza zuciyarta.

Tun a baya Cocin Ingila ya nemi afuwa kan alaƙarsa da cinikin bayi. Tarihi ya nuna cewa, wasu rassanta sun mallaki gonakin da Bayi ke aiki a yankin Caribbean, wasu limamai sun mallaki Bayi, sannan cocin ya karɓi gudunmawa daga masu cinikin bayi.

Shekaru uku da suka gabata ne aka amince da kafa wannan asusun bayan wani bincike ya gano cewa, wasu daga cikin tsoffin jarin cocin sun taɓa kasancewa a kamfanin da ke safarar bayi.

Manufar asusun shi ne; tallafa wa bincike, zuba jari da shirye-shiryen raya al’ummomin da cinikin bayi ya shafa.

Sai dai shirin ya fuskanci suka daga wasu, in da masu adawa ke cewa akwai muhawara kan irin rawar da cocin ya taka a tarihi, yayin da wasu kuma ke nuna damuwa kan batutuwan doka da kuma manufar biyan diyya.

A nata ɓangaren, Ghana na ci gaba da jagorantar kira ga ƙasashe da cibiyoyin da suka amfana daga cinikin bayi da su ɗauki nauyin biyan diyya ga al’ummomin da abin ya shafa.

Ministan Harkokin Wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya yabawa matakin shugabar Cocin Ingila, ya na mai cewa, wannan ziyara za ta ƙara ƙarfafa kira ga masu neman a amince da laifukan tarihi tare da ɗaukar matakan gyara.

Ya ƙara da cewa, addinin Kiristanci da aka kawo Afirka ya na koyar da cewa babu cikakkiyar ceto ba tare da amincewa da kuskure da kuma neman gyara ba.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

10 Comments

  1. Josh983

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/lPoYF

  2. Hailey2730

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/Xr39c

  3. Bernadette4703

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/w5ASh

  4. Timothy1815

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/qwfz8

  5. Jorge4989

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/d3eri

  6. Gideon2324

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/XohpS

  7. Declan1829

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/NWole

  8. Marshall3936

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/otELA

  9. Tori2081

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/f5ZwA

  10. Lewis3048

    02/08/2026

    https://shorturl.fm/DEmwm

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An