Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Tsimi Da Tanadi

Elon Musk Ya Zama Mutum na Farko da Arzikinsa Ya Kai Tiriliyan Ɗaya na Dala a Duniya

Mujallar kasuwanci ta Forbes ta bayyana attajirin nan na Duniya, Elon Musk, a matsayin mutum na farko da ya kai arzikin da ya haura Tiriliyan Ɗaya na Dalar Amurka. Wannan na zuwa ne bayan da kamfanin sararin samaniya na SpaceX ya fara kasuwanci a kasuwar hannayen jari ta Nasdaq.

Rahotanni sun nuna cewa, an fara sayar da hannun jarin SpaceX kan Dala 150 a kowace Haja, lamarin da ya bai wa kamfanin darajar kasuwa da ta kusan kai Tiriliyan biyu na Dalar Amurka. A cewar Forbes, wannan ci gaba ya ƙara wa Musk dukiya sosai, in da aka ƙiyasta yawan arzikinsa ya kai kusan Tiriliyan 1.1 na Dala.

Tun da farko dai, kafin fara cinikin hannun jarin SpaceX, an ƙiyasta cewa dukiyar Musk ta ƙaru da Dala Biliyan 188, in da ta kai kusan Dala Biliyan 982 bayan an sanya farashin hajojin kamfanin kan Dala 135 kowacce.

Ci Gaban Musk Daga Biliyan Zuwa Tiriliya

Elon Musk ya fara bayyana a jerin attajiran Duniya na Forbes a shekarar 2012, in da aka ƙiyasta dukiyarsa ta kai Dala Biliyan biyu kacal. A lokacin, shi ne mutum na 634 mafi arziki a Duniya.

Sai dai cikin shekaru tara kacal, ya zama mutum mafi arziki a Duniya a watan Janairun 2021, bayan da darajar hannayen jarin kamfanin Tesla ta yi tashin gwauron zabo, lamarin da ya sa ya zarce Jeff Bezos a matsayi na farko.

Muhimmancin Wannan Nasara

Mataimakin Editan Sashen Arziki na Forbes, Matt Durot, ya bayyana cewa, kai wa wannan mataki wani abin tarihi ne da a da ake ganin ba zai yiwu ba.

A cewarsa:

“Hawan Elon Musk zuwa arzikin Tiriliyan Ɗaya na Dala wani babban tarihi ne da ke nuna yadda za a iya samar da dukiya cikin sauri a duniyar da fasaha da haɗin kai suka mamaye.”

Ya ƙara da cewa, wannan nasara ta na nuna sabon babi a tarihin kasuwanci da harkokin ƙirƙire-ƙirƙire na Duniya.

Matsayin Forbes a Bibiyar Attajirai

Tsawon fiye da shekaru 40, Forbes na daga cikin manyan cibiyoyin da ke bibiyar arzikin manyan attajiran Duniya. Tun bayan ƙaddamar da jerin attajiran Duniya na farko a shekarar 1987, Mujallar ta tara bayanai masu yawa da bincike kan yadda attajirai ke samar da dukiyoyinsu da yadda arzikinsu ke sauyawa a tsawon lokaci.

Babban Jami’in Kula da Abubuwan Da Mujallar Forbes Ke Wallafawa, Randall Lane, ya bayyana cewa, babu wata kafar yaɗa labarai da ke da irin zurfin bayanai da amincewar da Forbes ta samu wajen bibiyar dukiyar attajiran Duniya.

Hasashen Musk Kan Makomar Fasaha

A wata tattaunawa ta musamman da Forbes ta yi da Elon Musk, ya yi hasashen cewa, Fasahar Ƙirƙirarriyar Basirar (AI) da Mutum-mutumin Robot (Robotic) za su sauya yanayin tattalin arzikin Duniya cikin shekaru kaɗan masu zuwa.

A cewarsa:

“Cikin shekaru biyar masu zuwa, basirar Dijital za ta zarce jimillar basirar dukkan Mutane. Haka kuma, ana iya samun Mutum-mutumin Robot masu kama da ɗan Adam Miliyan 100 ko ma Biliyan ɗaya.”

Elon Musk a yayin bikin Forbes Innovator 250 Celebration da aka gudanar a Palo Alto, tare da Kathleen Sheffer.

Musk ya kuma yi hasashen cewa, tattalin arzikin Duniya na iya ninkawa sau biyu cikin shekaru biyar zuwa shida masu zuwa, tare da manyan sauye-sauye da za su shafi rayuwa da kasuwanci a Duniya.

Madogara: Forbes.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

14 Comments

  1. Percy1406

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/PPny9

  2. Simon3259

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/PTc4l

  3. Kane340

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/BZmeH

  4. Hayes301

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/urzd9

  5. Alivia27

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/3Igtr

  6. Penelope1563

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/skh7y

  7. Beatrice4215

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/qd4Tq

  8. Adrian4013

    13/06/2026

    Последние новинки музыки 2026 скачать бесплатно – https://shorturl.fm/rrdv9

  9. Theo311

    13/06/2026

    Популярные песни 2026 скачать бесплатно https://shorturl.fm/rHNtJ

  10. Carla3918

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/uiJZj

  11. Reese1188

    13/06/2026

    Новинки музыки 2026 скачать бесплатно https://shorturl.fm/tunN9

  12. Heidi3175

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/vHxLU

  13. Lisa2294

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/a3Gyv

  14. Arthur1399

    13/06/2026

    https://shorturl.fm/jJ3OE

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Tsimi Da Tanadi

Sharhi: Tattalin Arziki

Tattalin Arziƙi (Economy) ya dogara ne a kan samar da Abinci, Sutura, Ayyuka, Kiwon Lafiya, Ilimi, Gine-Gine da sauransu, da
Tsimi Da Tanadi

Dabino na Samun Tagomashi a Saudiyya

Kasuwar Dabino a Saudiyya na bunƙasa, yayin da aka samu ƙaruwar riba da kashi 14% a shekarar da ta gabata