Taron wadda ya gudana a Jami’ar Bayero da ke Kano, ƙarƙashin shiryarwar Sashen Nazarin Harsunan Najeriya ta Jami’ar; tare da haɗin guiwar Sashen Ilimin Harsuna Ƙasashen Waje, da Sashen Taskace Tarihi, da Cibiyar Bincike da Nazarin Harsunan Najeriya da Fassara.
Taron ya mai da hankali ne kan asalin Baƙaƙen Hausa tun kafin zuwan rubutun A-ba-ja-da, watau – Tsarin rubutun Hausa na ainihi ba na Latin ko Ajami ba.
Wani masanin Harshen Hausa ɗanƙasar Jamhuriyar Nijar Dakta Korao Hamadou, ya gabatar da wasu haruffa waɗanda ya ce, su ne Baƙaƙen Hausa na asali tun kafin zuwan rubutun Ajami ko A-ba-ja-da na Turawa.
Ya gabatar da su ne a Maƙalar da ya gabatar a wajen wani Taron wuni guda da aka gudanar a ɗakin taro na CBN Centre da ke cikin Jami’ar Bayero (New Site) da ke jihar Kano.

Dr. Korao Hamadou ya na gabatar da maƙalarsa a taron.
A taron wadda ya samu halartar manyan Malamai, da Masana, da Manazarta, a kan Harshen Hausa daga sassa daban-daban na Duniya.

Mahalarta taron su na sauraron Dr. Korao Hamadou, a yayin da yake gabatar da maƙalarsa.
Har ila yau, Masanin daga Jami’ar Jamhuriyar Nijar, Dr. Korao Hamadou shi ne ya kasance Babban Baƙo mai jawabi, in da ya bayyana cewa, sabbin alamomin an samo su ne daga masu bayar da magungunan gargajiya (Magorai) ta hanyar taskace Saƙesaƙi, da Saiwoyi, da Ganyaye, da Kauci, da kuma Ɓawo.
Saboda haka, ya gabatar da waɗannan alamomi a gaban manyan malaman Harshen Hausa, ya kuma kafa hujja da cewar; irin waɗannan alamomi su ne na farko a wajen samar da rubutu a Duniya.
Hotunan Rubutun Hausa na Asali da Dr. Korao ya gabatar



Sannan, Masanin ya kawo sunayen manyan Littattafan Tarihi da na Musulunci da suke nuna cewa, lallai Hausawa ne suka fara samar da wani abin rubutawa da irin waɗannan alamomi.
Haka kuma, ya kawo misalai da dama a kan yadda za a yi amfani da Haruffan da yadda za su bunƙasa idan ana amfani da su.
Bugu da ƙari, manyan Malaman Harshen Hausa da na Tarihi sun taka muhawara da dama a kan waɗannan alamomi.

Wasu daga cikin manyan malamai mahalarta taron.
Ɗaya daga cikinsu, Farfesa Hamisu Miko Yakasai, ya ƙalubalanci Dakta Hamadou, a kan Haruffan ta yadda ba su samu sahalewar manyan Malaman Hausa ta hanyar gabatar da su ba.
Ya ƙara da cewa, “Idan ta hanyar masu bada Magani ko Itatuwa, da Kauci, da Ganye aka same su, to ai akwai tsoffin hanyoyi na sana’o’i irin su: Ƙira, Fawa, Rini, da Dukanci, to su kuma ina irin nasu suke?
An shafe tsawon lokaci ana tafka muhawara da kuma yi masa tambayoyi, yayin da shi kuma a dunƙule ya bada amsa da cewar wannan wani ɓangare ne na ilimi mai zurfi da haruffan suke ɗauke da shi, kuma ilimi sirri ne da shi, don haka bai kamata ya bayyana shi ba tun kafin lokacin ƙaddamar da shi ba.
Ya ce, a jira lokacin da za a ƙaddamar da shi, saboda akwai sauran nazari da bincike da yake yi kafin ya saki ilimin ga al’ummar Duniya.
Har wa yau, ana sa ran nan gaba za a yi wani taron Masana ilimin kimiyyar Harshe da Masana Tarihi da Al’adu, domin samar da matsaya a kan waɗannan alamomi.

