Ginin Dalar Masar ta zamanin da ba abu ba ne da kawai aka yi shi haka ba, ba tare da wasu dalilai ba, ko rashin ma’ana ko kuma an yi wannan katafaren gini na Dutse ne a matsayin Kabari ko hubbaren sarakuna domin girmama sarakunan na zamanin da ba.
Aiki ne da ya ƙunshi dalilai da dama kama daga jin-ƙai da addini da kuma falsafa waɗanda ta hanyarsu al’ummar ta Masar ke bayyana irin aƙidarsu ta addini da kuma yadda suka yi amanna da rayuwa bayan mutuwa.
Gina wannan Dala ba wai kawai nuni ne na ƙwarewa a fagen gini ba, abu ne da ya ƙunshi dalilai da dama, kamar yadda bayani ya gabata – rayuwar Duniya da addini da rayuwa bayan mutuwa.

Waɗannan gine-gine da dalilin yin su sun ɗauki hankalin mutane da dama tsawon ƙarni da dama. Wannan ne ma ya sa har ake ganin abin ya wuce tunani – inda ake danganta aiki da labarai iri daban-daban kan yadda aka samar da waɗannan dala-dala a Masar.
Wannan ne ya kai mu ga neman amsar wasu tambayoyi game da waɗannan abubuwan ban mamaki : Me ya sa Misirawa suka yi wannan gini da wannan siffa ta Dala domin adana gawarwakin sarakunansu? Mene ne amfanin waɗannan gine-gine ta fuskar addini da falsafa?
Shin ana amfani da Dalar ne a matsayin Kabari ko kuma su na da wata ma’ana ko dalili da ya shafi jana’iza?
Mutanen Masar ɗin ne kaɗai ko kuma akwai wasu mutanen da ke da hannu a aikin?
Sannan a ƙarshe an gina su ne ta hanyar aikin tilas ko kuma gwale-gwale, kamar yadda wasu ke iƙirari.
Bari mu yi nazarin wasu daga cikin dalilan gine-ginen dalar:
Ƙoƙarin kai wa ga Rana

Akan yi tambaya galibi cewa – Me ya sa sarakunan Masar na zamanin da suke son gina kaburburansu a siffar dala?
Ana ganin su na yin hakan ne domin nuna yadda suka yi amanna da bautar rana – wadda ita ce jigon bauta a zamanin da a Masar.
Su na yin wannan siffa ne musamman ma ƙoli-ƙolin Dalar – yadda yake da tsini – alama ce ta yadda hasken yake tunkaro Duniya. Saboda haka suke son binne sarakunansu a kabarin da yake da siffar yanayin hasken Rana, wadda suke fatan tashi zuwa gare ta a ranar tashin ƙiyama – kamar yadda tarihinsu addinin Masar ɗin na zamanin da ya nuna.
Hanyar zuwa Aljanna

Mutanen Masar su na kiran Dala “Mer” a harshensu na zamanin da – wanda hakan ke nufin wajen da za a tashi sama.
Wannan na nuna ƙarara abin da suka yi amanna da shi a lokacin cewa ta wannan Dala ne ruhin sarkinsu zai tashi ya tafi sama – Aljanna in da zai haɗu da Ubangiji Ra.
Mutanen Masar na zamanin da na ɗaukar Dala a matsayin hanyar zuwa rayuwa ta gaba – sama ko Aljanna – ga sarakunansu.
Saboda kamar su mutanen Masar na zaman da sun yi amanna cewa, Mutuwa ba ita ce ƙarshen rayuwa ba, sai ma dai farkon wata sabuwar rayuwa kuma hanyar tafiyar Ruhi zuwa ga Aljanna.
A don haka, su na ɗaukar Dala a matsayin wata matattakala ta kai wa ga sama – Aljanna.

Wasu masana sun yi amanna cewa, bayan alamtata da hasken Rana ita Dala wata alama ce ta ƙarfin da ke da nasaba da ubangiji – wanda wannan ƙarfi ne suka yi amanna zai ɗaga ruhin sarkinsu bayan ya rasu zuwa Aljanna.
Bayan rasuwarsa shi sarkinsu ya na zama abin da suke kira ‘Osiris’ – wato ubangijin bayan mutuwa – wanda ta hakan ya zama wanda ba zai mutu ba kuma kamar ubangiji, kuma abokin tafiya a tafiye-tafiyensa na yau da kullum a sama – Aljanna – saboda haka ne siffar Dala take haka.
Wannan ne ya sa a lokacin da su mutanen Masar suke gina Dala suke tsara ta, ta yadda za ta zama wajen ajiye gawar sarkin da ya mutu ba tare da wata matsala ba – domin kare ruhinsa ta yadda zai ci gaba da rayuwa da ba ta da ƙarshe.

A wajen al’ummar Masar ta wancan zamanin na da ruhi da kuma abokin tafiyarsa (Ba da Ka) ba za su iya tafiya zuwa rayuwa ta gaba da wadda ba ta da ƙarshe, ba tare da wajen adana jikin mutumin da ya mutu ba yadda zai kasance ƙalau ba tare da wani abu ya same shi ba.
Saboda haka ne suke yin wannan Dala su yi waje mai kyau da tsaro su tanadi kayayyakin da Sarki ya saba rayuwa da su a Duniya a ajiye masa a cikin wannan Dala da aka binne shi tare da adana gawarsa yadda ita ma ba za ta lalace ba ko a sace ta.
Su na yin hakan ne bisa amannar cewa, ruhin sarkin zai koma ya shiga jikinsa a lokacin da zai yi tafiya ta sama ko Aljanna wadda ba sauran mutuwa.
Akwai kuma wani tunanin cewa, in da ake danganta Dalar ta Masar da wata alamar ta Addini – wadda ke cewa, kafin a halicci ɗan’Adam da sauran halittu, Duniya Kogi ce da wani Tsauni a cikinsa.
Nazariyya ta ce, daga cikin wannan Tsauni ne Ubangijin Rana (Ra) kamar yadda suka yi imani ya halicci kansa da kuma sauran Duniya.
Bisa wannan ne suka yi amanna cewa, Dala alama ce ta wannan Tsauni na ainahi, saboda haka Misirawa na zamanin da suke ɗaukar Dala da tsarki da muhimmanci.

A nazarin da ta yi mai suna, “The Pharaohs in the Time of the God-Kings,” malamar Jami’a Claire Lalouette, ƴar Faransa ta bayar da shaida da wasu daga cikin rubuce-rubucen a kan tashin da sarkin ya yi zuwa Aljanna.
Ginin zuwa Aljanna

A rubutunsa na tarihin Masar ta zamanin da (“Ancient Egyptian History,” ) Ramadan Abdo ya yi ammana cewa hubbaren sarakunan lokacin ta zama haka ne – dala saboda abu biyu:
”Na farko domin girmamawa da tsarkake sarki – wanda saboda matsayinsa sai an gina masa ƙaton waje in da daga nan ne zai riƙa sanya ido a kan abin da ke faruwa a Duniya – kamar yadda yake yi a lokacin ya na raye a wannan duniyar.
”Abu na biyu kuma shi ne, sha’awar da al’ummar Masar na lokacin suke da ita ta yin abubuwa na al’ada na ƙawa – wannan ya sa su nemo wata hanya ta bajinta ta gina hubbare.
Sarakunan Masar sun gina Dala ne ta hanyar bautar da Mutane?

Wasu masana na ƙasashen Yammacin Duniya sun daɗe su na iƙirarin cewa, Bayi ne suka gina dala-dalar Masar – iƙirarin da ke nuna cewa, an ci zarafin Mutane a aikin gina dala-dalar da ta kasance gini mai ɗaukar hankali na ban mamaki a tarihin Duniya.
Sai dai kuma, wasu kayayyakin Tarihi da aka tono kwanan nan da wasu rubuce-rubuce da aka samu sun saɓa da wannan ra’ayi.

Kayayyakin sun nuna cewa al’ummar da aka santa da tsari da kuma ƙwarewa wadda kuma ke samar wa ma’aikatan manyan ayyuka irin su; Dala da tsari na kare rayuwarsu da kuma jin daɗin abin da ke nuna an damu da jin daɗinsu sosai.
Ga al’ummar Masar wannan dala-dala da kakanninsu suka gina a zamanin da, ba kawai manyan gine-gine ba ne a tsakiyar Sahara a wajen birnin.
Alamu ne na ci gaba da kuma tsabar kishin addini – da ke zaman hubbare, wajen ibada sannan kuma hanyar zuwa sama – Aljanna.
Har ila yau, sun kasance wurin yawon bude ido, in da al’umma daga sassa daban-daban na Duniya ke ziyarta.


