Al'amuran Yau Da Kullum

An Sace Munduwar Fir’auna a Gidan Tarihin Masar

Daga: Aliyu Adamu Tsiga

Hukumomin Masar sun ƙaddamar da gagarumin samame a sassan ƙasar bayan wani mai tsaurin-ido ya sace Munduwar Zinariya ta Fir’auna, mai shekaru 3,000 da aka adana a Gidan Adana Kayan Tarihin birnin Alƙahira.

Bayanai na cewa, wannan Munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita.

An rarraba hoton Munduwar Zinariyar ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da Filayen Jiragen Sama da Tashohin Jiragen Ruwa, da zummar daƙile fasaƙaurinta zuwa ƙetare.

Munduwar mai ɗauke da ado na musamman, na da matuƙar daraja tun zamanin Fir’aunan, yayin da ake danganta ta da tsoffin gumakan da aka yi bautar su a can baya, sannan an ce ta na da ƙarfin warkarwa.

Munduwar na cikin jerin kayayyakin tarihin da ake shirin zuwa da su wani gagarumin taron baje-kolin kayayyakin tarihi a Italiya da za a fara gudanarwa a watan gobe.

Tuni aka kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan sauran kayayyakin tarihin da ake da su a ƙasar domin tabbatar da cewa, suna nan daram.

Gidan tarihi na Masar shi ne mafi daɗewa a yanƙin Gabas ta Tsakiya, kuma ya na ɗauke da kayayyaki daban-daban har guda dubu 170.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An