Rana Kamar ta Yau – 24 ga Satumba, 1948

Motar farko na Honda.
A irin wannan Rana aka kafa Kamfanin Motoci na Honda (Honda Motor Co., Ltd.), wanda Injiniya Soichiro Honda ya assasa. Babban ofishin kamfanin ya na a Minato, Tokyo, Japan.
Tun daga 1946, Soichiro Honda ya kafa Cibiyar Binciken Fasaha ta Honda a kusa da Hamamatsu, in da ya fara ƙirƙira ƙananan Injina. Bayan shekaru biyu, an mayar da wannan buri babba ta hanyar kafa Honda Motor Co., Ltd. a hukumance.
Shekara guda bayan haka, a 1949, Honda ta ƙera baburinta na farko, wanda ya fara jan hankalin Duniya zuwa sabbin fasahar da kamfanin ke kawowa.
Me yasa aka kafa Honda?
Manufar Soichiro Honda ita ce; ƙirƙira sabuwar fasaha ta Injina da samar da Motocin da za su sauƙaƙa rayuwar al’umma, musamman ta hanyar samar da abin hawa mai arha, ingantacce, da sauƙin amfani.
Najeriya ta Shirya Komawa Mulkin Dimokraɗiyya – 1998

A Rana Mai Kamar Yau – 24 ga Satumba, 1998
Gwamnatin Soja ta Najeriya ta sanar da cewa ƙasar za ta koma mulkin Farar Hula a watan Mayu 1999, abin da ya zama muhimmiyar alama ta dawowa ga tsarin Dimokraɗiyya bayan shekaru masu yawa na mulkin soja.
Bayanin Yanayi
A wancan lokaci, Janar Abdulsalami Abubakar ne Shugaban Ƙasa bayan rasuwar Janar Sani Abacha a watan Yuni 1998.
Mutuwar Abacha ta buɗe sabon fata ga Najeriya, domin gwamnatin Abubakar ta ɗauki nauyin dawo da ƙasar kan tafarkin Dimokraɗiyya cikin gaggawa.
Muhimmancin 24 ga Satumba
A wannan Rana ce Gwamnatin ta bayyana a hukumance cewa za a gudanar da zaɓen Dimokraɗiyya a cikin watan Fabrairu 1999, sannan a miƙa mulki ga sabon Shugaban Ƙasa a watan Mayu. Wannan sanarwa ta saukar da nauyi daga zuƙatan al’umma, in da aka fara samun kwarin guiwa cewa Najeriya za ta fita daga Mulkin Soja.
Sakamakon Wannan Mataki
An gudanar da zaɓen 1999, in da tsohon Shugaban Soja, Olusegun Obasanjo, ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
A ranar 29 ga Mayu, 1999, aka rantsar da shi a matsayin Shugaban Ƙasa, abin da ya dawo da Najeriya kan tafarkin Dimokraɗiyya bayan kusan shekaru 16 na Mulkin Soja kai-tsaye.
Darasi a Tarihi
Wannan Rana ta 24 ga Satumba, 1998, ta zama alama ta sabon salo a tarihin siyasar Najeriya – daga Mulkin Soja zuwa Dimokraɗiyya, wanda har yanzu (2025)ake gudanarwa a Ƙasar.
Thabo Mbeki Ya Yi Murabus a Matsayin Shugaban Afirka ta Kudu – 2008
A Rana Mai Kamar ta Yau – 24 ga Satumba, 2008
Thabo Mvuyelwa Mbeki, Shugaban Afirka ta Kudu na biyu, ya yi murabus daga kan muƙaminsa bisa buƙatar jam’iyyarsa African National Congress (ANC).
Wanene Thabo Mbeki?

Thabo Mvuyelwa Mbeki, tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, da ya yi murabus.
- An haife shi a ranar 25 ga Yuni, 1942.
- Ya kasance Mataimakin Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Nelson Mandela daga 1994 zuwa 1999.
- Ya zama shugaban ƙasa daga 14 ga Yuni, 1999 har zuwa murabus ɗinsa a 24 ga Satumba, 2008.
Dalilan Murabus Ɗinsa
- Jam’iyyar ANC ta tilasta masa sauka daga mulki bayan dogon rikici da ya biyo bayan korar Jacob Zuma daga matsayin mataimakin Shugaban Ƙasa a 2005 kan zargin cin hanci.
- A makon kafin murabus ɗinsa, wani Alƙali ya yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi wa Zuma, tare da nuna cewa akwai hannun Siyasa a ciki. Wannan ya ƙara tunzura magoya bayan Zuma su matsa lamba kan Mbeki.
- Duk da cewa manufofin Mbeki na tattalin arziƙi sun ja hankalin masu zuba jari, rikicin cikin gida na Siyasa ya hana shi ci gaba da mulki.
Bayan Murabus
Bayan saukarsa, Kgalema Motlanthe ya karɓi ragamar mulki na wucin gadi kafin zaɓen 2009 wanda ya kai Jacob Zuma zuwa kujerar Shugaban Ƙasa.
Girgizar Ƙasa Mai Ƙarfi Ta Afku a Kudancin Pakistan – 2013

Girgizar Ƙasar Baluchistan, wani yanki mai yawan Hamada da Tsaunuka.
A Rana Irin ta Yau – 24 ga Satumba, 2013
Wata girgizar ƙasa mai ƙarfin awo 7.7 ta afku a kudancin Pakistan, in da ta ruguza ɗaruruwan Gidaje tare da kashe aƙalla Mutane 327.
Abin da ya Faru
Girgizar ta afku ne a lardin Baluchistan, wani yanki mai yawan Hamada da Tsaunuka masu tsauri.
Ƙarfin girgizar ya shafi ƙasashen Kudu maso Yammacin Asiya, in da aka ji girgizar har zuwa wasu sassa masu nisa.
Ɗaruruwan Gidajen Laka sun rushe kan mazauna yankin, abin da ya sa adadin mace-mace ya ƙaru da sauri.
Taimakon Gaggawa
Sojojin Pakistan sun tura ɗaruruwan Sojoji ta Jirgin Sama domin taimakon gaggawa.
An bayyana wannan a matsayin Girgizar Ƙasa mafi muni da ta afku a Kudancin Asiya tun shekarar 2005, lokacin da aka rasa rayukan kusan mutane 75,000 a Arewacin Pakistan.
Bala’in Hajji a Minna – 2015
A Rana Mai Kamar ta Yau – 24 ga Satumba, 2015
Wani mummunan turmutsutsi ya ɓarke yayin aikin Hajji a Minna, Makka, Saudiyya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Mutane sama da 1,100 tare da raunata 934. Wannan ya zama bala’in Hajji mafi muni a tarihin Saudiyya.

Gawarwakin wasu da suka rasu a turmutsutsin Aikin Hajjin 2013, a Minna.
Adadin Mutane da Aka Rasa
Adadin ya bambanta daga rahotanni daban-daban:
- Associated Press (AP): 2,411 sun mutu.
- Agence France-Presse (AFP): 2,236 sun mutu.
- Hukumomin Saudiyya (a hukumance, kwanaki biyu bayan faruwar lamarin): 769 sun mutu, 934 sun jikkata.
Ƙasashen da abin ya fi shafa
Mafi rinjaye sun fito daga Iran. Sannan daga wasu ƙasashe irin su Mali da Najeriya.
Muhimmancin Lamarin
Wannan bala’i ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka girgiza Duniya, in da aka yi kira da dama daga ƙasashe da ƙungiyoyin Duniya kan tabbatar da tsaro da ingantaccen tsarin gudanar da aikin Hajji a nan gaba.

