Tattalin arzikin Afirka na ci gaba da sauyawa sakamakon sabbin manufofin kasuwanci, zuba jari daga ƙasashen waje da kuma bunƙasar harkokin fasaha da masana’antu.
Wasu Ƙasashe sun fi jan ragamar ci gaban kasuwanci a nahiyar ta fuskar GDP (jimillar kuɗaɗen da Ƙasa ke samarwa na shekara), wanda hakan ke nuna ƙarfin tattalin arziki da tasirin su a harkokin kasuwanci na Duniya.
Ga Jerin Ƙasashen Afirka 10 Mafi Ƙarfin Tattalin Arziki
- 🇿🇦 Afirka ta Kudu – Dala Biliyan 410.3
- 🇪🇬 Masar (Egypt) – Dala Biliyan 347.3
- 🇩🇿 Aljeriya (Algeria) – Dala Biliyan 268.9
- 🇳🇬 Najeriya (Nigeria) – Dala Biliyan 188.3
- 🇲🇦 Maroko (Morocco) – Dala Biliyan 165.8
- 🇰🇪 Kenya – Dala Biliyan 131.7
- 🇪🇹 Habasha (Ethiopia) – Dala Biliyan 117.5
- 🇦🇴 Angola – Dala Biliyan 113.3
- 🇨🇮 Côte d’Ivoire – Dala Biliyan 88.3
- 🇬🇭 Ghana – Dala Biliyan 74.6
Madogara: Rahoton IMF 2025

