Bikin Irreecha, wani shahararren bikin al’ummar Oromo ne na ƙasar Habasha (Ethiopia), wanda ake gudanarwa duk shekara domin nuna godiya ga Ubangiji (Waaqaa) bisa ni’imar rayuwa, amfanin gona, da zaman lafiya.

Ana gudanar da bikin ne a ƙarshen Damina da farkon Bazara — lokacin da albarka ta yawaita, Gonaki suka yi kyau, kuma Mutane ke murnar sabuwar dama ta rayuwa.




Dubban jama’a daga sassa daban-daban na Habasha kan taru a wuraren ibada na gargajiya, musamman a bakin Tafkin Hora Arsadi a garin Bishoftu, in da ake yin addu’o’i, waƙe, raye-raye, da bukukuwan gargajiya cikin annashuwa da farin ciki.



Bikin Irreecha ya kasance alamar haɗin kai, zaman lafiya, da godiya, ya na ɗauke da saƙo mai ƙarfafa zumunci da mutunta al’ada — abin alfahari ga al’ummar Oromo da Habasha gaba ɗaya.


📷 Amensisa Ifa

