Al'amuran Yau Da Kullum

Ƙasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya na Samun Haɓakar Yawon Buɗe Ido

Ƙasashe da dama a Afirka da Gabas ta Tsakiya, ciki har da Maroko, Lebanon, Jordan, Masar (Egypt), Afirka ta Kudu, Angola da Habasha (Ethiopia), sun samu gagarumar nasara a ɓangaren Yawon buɗe ido a bara, in da aka samu ƙaruwa mai yawa a adadin baƙi daga ƙasashen Duniya.

Wannan ci gaba ya nuna yadda waɗannan ƙasashe ke sake ɗaukar sahun gaba a harkar Yawon buɗe ido ta Duniya.

Haɓakar Yawon buɗe ido ta samo asali ne daga zuba jari a Al’adu, Tarihi, Albarkatun Ƙasa, da manyan tarukan wasanni, kamar yadda AFCON ya ƙara yawan masu Yawon buɗe ido a Maroko, da yadda Habasha da sauran ƙasashe suka amfana daga manyan bukukuwa da taruka.

Yayin da ake tunkarar shekarar 2026, yawancin waɗannan Ƙasashe sun mayar da hankali kan faɗaɗa ababen more rayuwa, bunƙasa sabbin tsare-tsaren Yawon buɗe ido, da kuma bambanta irin abubuwan da suke bai wa baƙi, domin ci gaba da yin tagomashi.

Maroko: Tarihi, Yanayi da Manyan Taruka Sun Haɓaka Yawon Buɗe Ido

Maroko ta samu ƙaruwa da haɓaka fannin a Yawon buɗe ido, in da aka samu ƙaruwa a adadin baƙi daga Afirka, Turai da Arewacin Amurka. Wannan ci gaba ya samo asali ne daga haɗa tsohon tarihi, birane masu armashi kamar Marrakech, Fez da Rabat, da kyawawan yankunan Bakin Teku.

Baya ga abubuwan gargajiya, manyan tarukan wasanni kamar AFCON (2025) sun ƙara jawo masu Yawon buɗe ido, in da baƙi suka zo kallon gasar kuma suka ziyarta wuraren Yawon shaƙatawa a Ƙasar.

Maroko na bunƙasa sabbin hanyoyin Yawon shaƙatawa yayin da take haɓaka ababen more rayuwa, Otal-Otal, hanyoyin sufuri da tsaro, domin ci gaba da jan hankalin baƙi. Wannan ya tabbatar da cewa, Maroko na cikin jerin manyan wuraren Yawon buɗe ido a Afirka da Gabas ta Tsakiya, tare da haɗa tarihi, al’adu, yanayi da wasanni.

Masar (Egypt): Tarihi da Zamani Sun Haɗu

A shekarar 2025, Masar ta samu ƙaruwa da kashi 21% na baƙin Yawon buɗe ido daga Janairu zuwa Satumba idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wanda ya kai kusan baƙi Miliyan 19. Wannan nasara ta samo asali ne daga; Inganta tsaro, faɗaɗa shirye-shiryen Yawon buɗe ido, amfani da fasahar zamani wajen sabunta wuraren tsohon tarihi da wuraren shaƙatawa.

Zirga-zirgar jiragen Yawon shaƙatawa (Charter flights) ta ƙaru da kashi 32%, yayin da sabon birnin New Alamein City ya samu ƙaruwa ta musamman da kashi 450%. Haka nan, Babban Gidan Tarihin Masar (Grand Egyptian Museum) na ci gaba da jan hankalin matafiya, wanda ke tabbatar da cewa Yawon buɗe ido zai ci gaba da zama muhimmin ginshiƙi na Tattalin Arziki.

Lebanon: Farfaɗowa Duk da Ƙalubale

Lebanon ta samu ƙaruwa da kashi 22% a Yawon buɗe ido a 2025, duk da ƙalubalen Siyasa da Tattalin Arziki. Baƙi sun fara dawowa wurare kamar Beirut da Kwarin Bekaa (Bekaa Valley) domin jin daɗin al’adu, tarihi da abinci. Filin jirgin saman Beirut ya nuna alamun farfaɗowa sosai, yayin da wuraren tarihi, dazuzzukan Al Shouf Cedar Forest da tsoffin gine-gine ke ci gaba da jan hankalin baƙi, musamman ƴan Lebanon mazauna ƙasashen waje da baƙi daga Gulf.

Jordan: Tarihi da Masarauta

Jordan ta samu ƙaruwa da kashi 11% na baƙi daga Janairu zuwa Satumba 2025. Manyan wurare kamar Petra da Jerash sun ƙara jan hankalin matafiya, musamman masu sha’awar tarihi da Hawan Tsaunuka da Kwari (Hikers). Yawan baƙin da ke kwana a Ƙasar ya kai Miliyan 2.7 zuwa tsakiyar shekara.

Inganta zirga-zirgar Jiragen Sama da bunƙasa ababen more rayuwa a wurare kamar Aqaba sun ƙara armashi ga yawon buɗe ido a Jordan.

Angola: Sabuwar Ƙasa Mai Tasowa

Angola ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi saurin haɓaka a Yawon buɗe ido, in da ta samu ƙaruwa da kashi 30% daga Janairu zuwa Satumba 2025—mafi girma a yankin.

Duk da cewa har yanzu ana gina ababen more rayuwa, Angola na jan hankalin baƙi ne ta hanyar kyawawan albarkatun halitta, da birane masu tasowa kamar Luanda.

Haka nan, sauƙaƙa Biza da shigowar manyan Kamfanoni da Otal-Otal sun ƙara ƙarfafa wannan ci gaba.

Habasha (Ethiopia): Arzikin Al’adu da Kyawawan Halittu

Habasha ta samu ƙaruwa da kashi 18% a Yawon buɗe ido a 2025. Tsohon tarihinta, irin su Coci-cocin Lalibela, da kyawawan wuraren halitta kamar Dutsen Simien, sun jawo hankalin baƙi daga Turai, Arewacin Amurka da sauran ƙasashen Afirka.

Faɗaɗa hanyoyin Jiragen Sama da inganta ababen more rayuwa sun sauƙaƙa isa wuraren Tarihi, yayin da Gwamnatin Ƙasa ke tallata al’adu da yanayi a Duniya.

Afirka ta Kudu: Ƙasa Mai Bambancin Yawon Buɗe Ido

Afirka ta Kudu ta samu ƙaruwa da kashi 17% na baƙi a 2025. Daga biranen Cape Town da Johannesburg, zuwa Gandun Daji da wuraren kiwon Dabbobi, Ƙasar na ba da gogewa iri-iri ga matafiya.

Baya ga wuraren Namun Daji, Abinci gargajiya da Barasa (Wine Tourism) da faɗaɗa hanyoyin Jiragen Sama sun ƙara armashi ga Ƙasar.

Kenya: Birane, Balaguro da Kasuwanci Sun Haɓaka Yawon Buɗe Ido

Kenya ta samu ƙaruwa a harkar Yawon buɗe ido, musamman a lokacin bukukuwa, in da aka tsara kusan kujeru 470,000 a Jiragen cikin gida. Wannan ci gaba ya samo asali ne daga ƙaruwa a balaguron bukukuwa da buƙatar kasuwanci, musamman tsakanin biranen Nairobi da Mombasa.

Kenya na jan hankalin matafiya ta hanyoyi daban-daban: yanayi mai kyau, shahararrun wuraren yawon shaƙatawa kamar Maasai Mara, da tsaunukan Aberdare da Bakin Teku na Mombasa, da kuma gogewar kasuwanci da Taron Bajekoli. Wannan haɗin na Yawon shaƙatawa da harkokin kasuwanci ya tabbatar da cewa Kenya na matsayin Cibiya mai muhimmanci ga Yawon buɗe ido da kasuwanci a Gabashin Afirka.

Tanzaniya: Yanayi da Wuraren Shakatawa Sun Ƙara Jawo Baƙi

Tanzaniya ta samu babban haɓaka a Yawon buɗe ido, in da yawan kujerun Jiragen cikin gida ya ƙaru zuwa sama da 415,000. Wannan ya nuna ƙaruwar buƙatar Yawon buɗe ido, musamman zuwa wurare irin su: Zanzibar, Serengeti da Kilimanjaro, da kuma ingantacciyar hanyar sadarwa tsakanin biranen Dar es Salaam da Arusha.

Tanzaniya na jan hankalin matafiya ba kawai don Yawon shaƙatawa ba, har ma don kasuwanci da tarurrukan Bajekoli, wanda ya haifar da ƙarin buƙatu ga jiragen cikin gida, hakan na nuna harkar Jiragen sama zuwa sabon mataki.

Aljeriya: Haɗin Kai da Birane Sun Ƙarfafa Yawon Buɗe Ido

Aljeriya ta samu ci gaba a Yawon buɗe ido, inda aka tsara kujeru sama da 388,000 a lokacin bukukuwa. Girman ƙasar da buƙatar haɗin kai tsakanin birane ya ƙarfafa wannan haɓaka, yayin da Kamfanoni Jiragen Sama ke ƙoƙarin samar da sabbin hanyoyin sufuri na cikin gida.

Aljeriya na jan hankalin baƙi ta hanyar kyawawan wuraren tarihi, dazuzzukan Sahara, da biranen Algiers, Oran, Constantine, Setif, Tlemecen, dss, wanda ke haɗa tarihi da yanayi.

Sabbin hanyoyin jiragen sama na tabbatar da cewa Ƙasar na ƙara zama wurin yawon buɗe ido mai jan hankali a Afirka ta Arewa.

Tsare-tsaren Yawon Buɗe Ido da Hasashen 2026

Haɓakar Yawon buɗe ido da aka samu daga Janairu zuwa Satumba 2025 ta nuna juriya da sabbin dabaru da ƙasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya suka ɗauka.

Yayin da ake kallon 2026, yawancin ƙasashe sun tsara:

  • Faɗaɗa ababen more rayuwa,
  • Bunƙasa yawon buɗe ido mai dorewa (eco-tourism),
  • Janyo masu zuwa hannun jari.

Waɗannan tsare-tsare na nufin ƙara inganta jin daɗi da walwalar baƙi, tare da tabbatar da dorewar ci gaban fannin.

Kammalawa

Ƙasashe kamar Maroko, Lebanon, Jordan, Masar, Afirka ta Kudu, Angola da Habasha sun shiga wani sabon babi na ci gaba a fannin Yawon buɗe ido a Afirka da Gabas ta Tsakiya. Wannan gagarumar haɓaka ta nuna yadda amfani da tarihi, al’adu, albarkatun ƙasa da yanayi ke ɗaga darajar Ƙasa a idon Duniya.

Ta hanyar zuba jari a ababen more rayuwa, ƙirƙira da fasaha, da bambanta nau’o’in Yawon buɗe ido, waɗannan Ƙasashe na shirin ƙarfafa matsayinsu a matsayin manyan wuraren Yawon buɗe ido na Duniya yayin da aka tunkari 2026.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An