Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'ada

Yadda Bikin Murnar Sabuwar Shekarar Amazigh Ya Gudana

Al’ummomin Amazigh (Berber) a faɗin Arewacin Afirka (Maghreb), musamman a (Maroko, Aljeriya, Tunisiya, Libya da wasu sassan Masar) na gudanar da bikin Yennayer, wato sabuwar shekararsu ta Gargajiya; wannan biki ya na nuna farkon shekarar 2976 a Kalandar Amazigh.

Yennayer Biki ne mai tushe tun zamanin da, wanda yake da alaƙa kai-tsaye da Noma da albarkar Ƙasa, domin ya na nuna sabuwar shekarar yin shuka da fatan samun albarka.

A al’adance, ana gudanar da bukukuwa, shiga ta al’ada, waƙe-waƙe, kaɗe-kaɗe, raye-raye, cin abinci, tarurrukan iyalai, da addu’o’in samun albarkar Amfanin Gona.

Baya ga kasancewarsa Biki na Noma, Yennayer alama ce ta ainihin asalin ƙabilar Amazigh, wadda ke nuna jajircewarsu wajen kare Harshe, Tarihi da al’adunsu.

Wannan Biki na da muhimmanci matuƙa, saboda al’ummar Amazigh sun shafe ƙarni su na fuskantar tawayar Harshe da al’adu. Tun karni na bakwai, lokacin da mamayan Larabawa suka shigo Arewacin Afirka, harshen Larabci da addinin Musulunci suka mamaye tsarin hukuma, yayin da harsunan Amazigh suka fuskanci koma baya.

Sai dai, sakamakon jajircewar masu fafutukar kare al’adun Amazigh, an samu gagarumin ci gaba a shekarun baya-bayan nan.

A 2011, Maroko ta amince da Tamazight a matsayin harshen hukuma. Haka kuma, Aljeriya (2017) da Maroko (2023) sun ayyana Yennayer a matsayin ranar hutu ta Ƙasa.

Saboda haka, Yennayer ba kawai murnar bikin sabuwar shekara ba ce, alama ce ta nasara, gwagwarmaya, juriya, da doguwar fafutukar al’umma wadda ta kai Amazigh ga nasara.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'ada

Bikin Guérewol na Ƙabilar Wodaabe a Jamhuriyar Nijar

Bikin Guérewol wata gasa ce ta al’adar neman aure da ake yi a kowace shekara tsakanin al’ummar Wodaabe Fula na
Al'ada

Shin Kayan Lefe Kyakkyawa ko Mummunar Al’ada Ce?

Abdulmutallib A. Abubakar malami a sashen nazarin aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Barno kuma mai sharhi kan