Sabon rahoton shekara-shekara na Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa, duk da manyan sauye-sauyen tattalin arziki da Gwamnatin Najeriya ta aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata, talauci da matsalar rashin wadataccen Abinci sun ci gaba da ƙaruwa.
A cewar rahoton, kimanin kashi 63% na ƴan Najeriya su na rayuwa a ƙarƙashin matakin talauci na ƙasa. Haka kuma, sama da mutum Miliyan 27 sun fuskanci matsalar rashin wadataccen Abinci a ƙarshen shekarar 2025.
Sauye-sauyen Da Aka Yi
IMF ya yabawa Gwamnatin Najeriya kan wasu manyan matakai da ta ɗauka, waɗanda suka haɗa da:
- Cire tallafin Man Fetur
- Sauya tsarin musayar Kuɗi (Naira)
- Dakatar da biyan giɓin kasafin Kuɗi ta hanyar buga Kuɗi
- Tsaurara manufofin Kuɗi domin rage hauhawar farashi
A cewar IMF, waɗannan matakai sun taimaka wajen ƙarfafa tattalin arziki da dawo da kwarin guiwar masu zuba jari.
Amma Me Ya Sa Talauci Ke Ƙaruwa?
Rahoton ya nuna cewa duk da kyautatuwar wasu alamomin tattalin arziki, rayuwar Talakawa ba ta inganta yadda ake fata ba. Hauhawar farashin kayayyaki, musamman Abinci da makamashi, ta rage ƙarfin sayen jama’a.
Har ila yau, matsalolin tsaro sun ci gaba da shafar Noma da samar da Abinci a sassa daban-daban na ƙasar.
Abubuwan Da Suka Inganta
Rahoton ya lura da wasu ci gaba masu muhimmanci:
- Tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kusan 4% a 2025
- Ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ta ƙaru daga dala Biliyan 40 zuwa Biliyan 46
- Naira ta samu ɗan ƙarfi idan aka kwatanta da Dala a wasu lokuta
- An samu ƙarin masu zuba jari daga ƙasashen waje
Matsalar Bashin Gwamnati
Duk da waɗannan nasarori, IMF ya nuna damuwar cewa, kuɗin ruwa da Gwamnatin Tarayya ke biya kan basussuka ya kai kusan kashi 53% na kuɗaɗen shiga a shekarar 2025. Wannan na nufin sama da rabin abin da Gwamnati ke samu ya na tafiya ne wajen biyan bashin da ake bin ta.
Tallafin Kuɗi Ga Talakawa
IMF ya ba da shawarar a faɗaɗa shirin tallafin Kuɗi kai-tsaye ga marasa galihu.
Rahoton ya kuma nuna cewar, an yi wa iyalai miliyan 9.2 rajista a cikin tsarin tallafin, ƙasa da burin da Gwamnati ta sa na kai wa ga iyalai Miliyan 15.
Haka kuma, yawancin waɗanda suka amfana sun karɓi tallafin ne sau uku kacal tun bayan ƙaddamar da shirin a shekarar 2023.
- Gwamnati ta yi niyyar kai tallafin kuɗi ga gidaje (iyalai) miliyan 15
- Amma zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, Iyalai (Household) Miliyan 9.2 ne kawai aka yi wa rajista.
- Haka kuma, yawancin waɗanda suka amfana sun karɓi tallafin ne sau kaɗan (kimanin sau uku) tun bayan fara shirin.
Abin Da IMF Ke Ba Najeriya Shawara
Rahoton ya buƙaci Najeriya ta:
- Ƙara saka jari a Noma , Ilimi da Lafiya
- Inganta samar da Wutar Lantarki da ababen more rayuwa
- Ƙarfafa shirye-shiryen tallafawa marasa galihu
- Ci gaba da yaƙi da hauhawar farashi
- Magance matsalolin tsaro da ke hana bunƙasar tattalin arziki.
Rahoton IMF ya nuna cewa, akwai bambanci tsakanin bunƙasar tattalin arziki a takardu da kuma yanayin rayuwar jama’a a zahiri. Duk da cewa wasu manyan alamomin tattalin arziki su na nuna ci gaba, amma miliyoyin ƴan Najeriya har yanzu su na fama da tsadar rayuwa, rashin wadataccen Abinci da talauci.
Babban ƙalubalen da ke gaban Gwamnati shi ne; yadda za a tabbatar cewa, amfanin sauye-sauyen tattalin arziki ya kai ga talakawan Ƙasa, ba wai ya tsaya ga alƙaluman tattalin arziki kawai ba.


Zachary3296
14/06/2026https://shorturl.fm/IAPp5
Roland1182
14/06/2026https://shorturl.fm/TlBLx
Alfred3963
14/06/2026https://shorturl.fm/k1Ufn
Valentina2199
14/06/2026https://shorturl.fm/Trdtp
Tyler612
14/06/2026https://shorturl.fm/dLcP2
Joseph2269
14/06/2026https://shorturl.fm/9rSXa
Jared4654
14/06/2026https://is.gd/ee7ro6
Liam3908
14/06/2026https://is.gd/1n94DI
Frank669
14/06/2026https://shorturl.fm/qd4Tq
Seth2411
14/06/2026https://shorturl.fm/qd4Tq
Rory4081
14/06/2026https://shorturl.fm/dOllV
Zoey2243
14/06/2026https://shorturl.fm/pMvy9
Fiona3376
14/06/2026https://shorturl.fm/TzbTi
Ray2357
14/06/2026https://shorturl.fm/2Yhqp
Miriam4968
14/06/2026https://shorturl.fm/ZjaHh
Bob2755
14/06/2026https://shorturl.fm/GIdac
Miguel4169
14/06/2026https://shorturl.fm/JFcSC
Daisy3650
14/06/2026https://shorturl.fm/NfHS6
Nikita2535
14/06/2026https://shorturl.fm/IVoiT
Anthony4183
14/06/2026https://shorturl.fm/Nrdno
Chandler890
14/06/2026Последние новинки музыки 2026 скачать бесплатно – https://shorturl.fm/rrdv9
Penelope4212
14/06/2026https://shorturl.fm/81ECL
Aliyah830
14/06/2026Популярные песни 2026 скачать бесплатно https://shorturl.fm/DXlpZ
Claudia4935
14/06/2026https://shorturl.fm/WusC1
Maxwell1792
14/06/2026https://shorturl.fm/EqLU2
Monica621
14/06/2026https://shorturl.fm/qVUkN
Jerry727
14/06/2026https://shorturl.fm/wN7wd
Brittany84
14/06/2026https://shorturl.fm/vYi4Z
Melody1005
14/06/2026https://shorturl.fm/7iplG
Lane3109
14/06/2026Последние новинки музыки 2026 скачать бесплатно https://shorturl.fm/naLA6
Kathryn4114
14/06/2026https://shorturl.fm/d25No
Anna2208
14/06/2026https://shorturl.fm/tInhx
Payton270
14/06/2026https://shorturl.fm/Ma8CL