Kuɗi na daga cikin muhimman ginshiƙai da ke nuna ƙarfin tattalin arzikin kowace Ƙasa. Ƙarfin Kuɗi na nuni da ƙarfin ikon saye, amincin masu zuba jari da kuma kyakkyawan tsarin manufofin Ƙasa.
A cikin watan Agusta 2025, Mujallar Forbes ta fitar da jerin ƙasashen Afirka 10 da ke da kuɗaɗen da suka fi ƙarfi idan aka kwatanta da Dalar Amurka.
Jerin Ƙasashen
- São Tomé and Príncipe 🇸🇹
- 1 USD = 22,282 Dobras (STN)
Ƙasar tsibiri ce a Tekun Atlantika, tattalin arzikinta ya dogara da albarkatun Man Fetur, da yawon buɗe ido.
- Saliyo 🇸🇱
- 1 USD = 20,970 Leones (SLL)
Duk da tarihin Yaƙin Basasa, ƙasar na farfaɗowa ta fuskar tattalin arziki musamman wajen haƙar ma’adinai.
- Guinea 🇬🇳
- 1 USD = 8,676 Guinean Francs (GNF)
Sananniya ce wajen haƙar ‘Bauxite’ (wanda ake sarrafa aluminum), wanda ke kawo kuɗaɗen shiga.
- Uganda 🇺🇬
- 1 USD = 3,549 Ugandan Shillings (UGX)
Tattalin arzikinta ya dogara da Noma, da Kofi, da kuma Man Fetur.
- Burundi 🇧🇮
- 1 USD = 2,983 Burundian Francs (BIF)
Ƙasa ce ƙarama, amma mai ƙarfin tattalin arzikin Noma.
- Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo (DRC) 🇨🇩
- 1 USD = 2,903 Congolese Francs (CDF)
Ƙasa mai yalwar albarkatun ƙasa, musamman ‘Cobalt’ da ‘Coltan.’
- Tanzaniya 🇹🇿
- 1 USD = 2,505 Tanzanian Shillings (TZS)
Ƙasar yawon buɗe ido, musamman Serengeti da Kilimanjaro, da tsibirin Zanzibar, da kuma ma’adinai kamar Zinariya.
- Malawi 🇲🇼
- 1 USD = 1,734 Malawian Kwachas (MWK)
Tattalin arzikinta ya ta’allaka kan Noma, musamman Taba da Masara.
- Najeriya 🇳🇬
- 1 USD = 1,531 Nigerian Naira (NGN)
Babbar ƙasa ce ta tattalin arzikin Afirka, ta dogara da Man Fetur, amma ta na fama da matsalar hauhawar farashi.
- Rwanda 🇷🇼
- 1 USD = 1,445 Rwandan Francs (RWF)
Ƙasa mai tasowa da saurin ci gaba, musamman a fannin fasaha, tsaftar muhalli da yawon buɗe ido.
Abin da Wannan Ke Nunawa
Ƙasashen da suka fi ƙarfi wajen kuɗi su na nuna:
- Tsayayyen tsarin tattalin arziki.
- Kyakkyawan amfani da albarkatun ƙasa.
- Ingantattun manufofin Gwamnati.
Sai dai kuma, ƙarfin Kuɗi shi kaɗai ba ya nuna wadatar al’umma gaba ɗaya, domin akwai ƙasashe da ke da ƙarfi wajen Kuɗi amma tattalin arzikin jama’a ba ya haɓaka sosai ba.
Wannan jeri ya nuna irin yadda ƙasashen Afirka ke ƙoƙarin tabbatar da daidaito a tattalin arzikinsu.

