Jiya Da Yau

Lina Medina: Uwa mafi ƙanƙantar shekaru a Duniya

A tarihin bil’adama akwai labaran da suka ƙunshi mamaki, wasu kuma su na ɗauke da darussa masu zurfi. Labarin Lina Medina, yarinya daga ƙasar Peru, na ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa da ba a manta da su ba.

Farkon Rayuwa da Samuwar Ciki

An haifi Lina Medina a shekara ta 1933 a ƙauyen Ticrapo, cikin gundumar Castrovirreyna Province a ƙasar Peru. Mahaifinta, Tiburelo Medina, ya kasance mai sana’ar sarrafa Azurfa, yayin da mahaifiyarta ita ce Victoria Losea. Lina ta kasance ɗaya daga cikin ƴaƴa tara a cikin iyalin iyayenta.

Lokacin da take da shekaru biyar, iyayenta suka kai ta Asibiti a garin Pisco, saboda ciki ya fara fitowa a jikinta. A farko Likitoci sun ɗauka cutar ciwon ƙari (tumor) ce, amma daga ƙarshe suka gano ta na da ciki, har ma cikin ya kai wata bakwai. Likita Dr. Gerardo Lozada, wanda daga baya ya kula da ita, ya tabbatar da hakan tare da sauran ƙwararru daga Lima.

Lamarin ya jawo hankalin Duniya. Jaridar San Antonio Light ta Amurka ta wallafa a ranar 16 ga watan Yuli, 1939, cewa ƙungiyar Likitoci a Peru ta buƙaci a kai Lina Cibiyar Haihuwa ta Ƙasa. Har ma aka rawaito cewa, wani kamfanin shirya Fina-finai daga Amurka ya ba da tayin Dala 5,000 domin ya samu damar yin Fim ɗin lamarin, amma iyayenta suka ƙi amincewa.

Likita Lozada da kansa ya yi rikodin Fim ɗin haihuwar don amfani a fannin binciken kimiyya, in da ya gabatar da shi a gaban Majalisar Likitocin Peru.

Haihuwa da Abubuwan Mamaki

Bayan makonni shida da gano ta na da ciki, a ranar 14 ga Mayu, 1939, Lina ta haihu ta hanyar aikin tiyata (caesarean section) saboda ƙananan ƙashin ƙugunta ba zai iya ba ta damar haihuwa ta hanyar ɗabi’a ba. Tiyatar ta gudana ne a hannun Dr. Lozada da Dr. Busalleu, tare da Dr. Colareta a matsayin mai bada maganin sa Barci.

An haifi jariri Namiji mai nauyin Kilo 2.7, aka kuma saka masa suna “Gerardo,” (sunan likitan da ya kula da lamarin). Likitoci sun tabbatar cewa Lina ta ri ga ta sami cikakken tsarin gaɓoɓin Mace saboda abin da ake kira ‘precocious puberty’ (balaga tun da wuri).

Lokacin da Lina Medina ta haifi ɗanta, ta na ƴar shekaru biyar.

Likita Edmundo Escomel ya wallafa rahoton nata a cikin Mujallar likitanci ta Faransa, ‘La Presse Médicale,’ in da ya bayyana cewa, al’adarta ta farko ta zo tun ta na watanni takwas, saɓanin rahotannin baya da suka nuna wai ta fara al’ada tun ta na shekaru biyu da rabi ko uku.

Rayuwar Gerardo

Lina Medina tare da ɗanta Gerardo.

Da farko an shaidawa Gerardo cewa, Lina ƴar’uwarsa ce, amma daga baya, lokacin da ya kai shekaru goma, ya gano cewa ita ce mahaifiyarsa. Bayan wani lokaci, Likita Lozada ya ɗauki nauyin tarbiyyar Gerardo a gidansa a Lima, in da ya kuma ba da damar Lina ta zauna da yin aiki a asibitinsa. Duk da haka, ba ta samun damar ganin ɗanta akai-akai.

Lina Medina tare da ɗanta Gerardo.

Gerardo ya tashi cikin ƙoshin lafiya, amma daga baya ya rasu a shekara ta 1979, ya na da shekaru 40, sakamakon cutar ƙashi (bone marrow disease).

Batun Mahaifin Jariri

A bisa dokar ƙasar Peru, kasancewar Lina ta ɗauki ciki a wannan ƙanƙantar shekaru ya nuna cewa ta fuskanci cin zarafi. Duk da haka, har zuwa yau ba a san asalin mahaifin jaririn ba.

Lina ba ta taɓa bayyana yadda lamarin ya faru da ita ba, kuma wasu sun ce; wataƙila ma ba ta sani ba saboda ƙarancin shekarunta a wancan lokacin.

Mahaifinta, an kama shi bisa zargin cin zarafi, amma daga baya aka sake shi saboda rashin shaida da hujja.

Rayuwa daga Baya

Bayan wannan lamari, Lina ta ci gaba da rayuwa cikin natsuwa da ɓoye sirri. A lokacin samartaka, ta yi aiki a matsayin Sakatariya a Asibitin Dr. Lozada a Lima, abin da ya ba ta damar samun ilimi da kuma tallafawa ɗanta ya yi karatu har zuwa Sakandire.

A shekara ta 1972, ta yi aure kuma ta haifi ɗa na biyu. Amma duk da shaharar da ta samu a Duniya, ta ƙi bayyana cikakkun bayanai game da abin da ya faru da ita.

Lina Medina lokacin da ta yi aure.

A shekara ta 2002, ta ƙi ba da bayani ga Kamfanin Dillanci Labarai na Reuters, kamar yadda ta saba ƙin amsa tambayoyin manema labarai tun a baya.

Darasin Tarihi ga Al’umma

Labarin Lina Medina ya koya mana darussa masu yawa:

Ƙaddara: A wasu lokuta abubuwan da ba mu zato ko tsammani ba ne suke faruwa a rayuwarmu.

Kare Yara: Ya na nuna muhimmancin tsare lafiyar yara da kare su daga cin zarafi.

Kimiyya: Ya na bayyana yadda ilimin Likitanci ke iya fassara abin da ake ɗauka a matsayin al’ajabi, amma har yanzu akwai ɓangaren rayuwa da ya wuce iyakokin fahimtar Ɗan’Adam.

Sirri da natsuwa: Duk da wannan shahara, Lina ta zaɓi rayuwa cikin sauƙi da ɓoye sirri, abin da ke koya mana darasin mutuntaka da muhimmanci adana sirri.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Jiya Da Yau

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne
Jiya Da Yau

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen