Al'amuran Yau Da Kullum

Yadda Aka Gudanar da Bikin Ranar Hausa ta Duniya a Garin Daura

Taron Ranar Hausa ta Duniya 2025, da ya gudana a garin Daura na Jihar Katsina, ya kasance abin tarihi da ya ƙaraɗe Duniya, domin kowane lungu da saƙo ya ji ɗuriyar wannan rana ta musamman.

Ranar ta kasance wata muhimmiyar rana ce da aka ware domin tunawa da harshen Hausa, al’adunsa da kuma tasirinsa a fagen rayuwa ta yau da kullum.

An fara karrama wannan rana tun shekarar 2015, inda aka mayar da ita matsayin biki na shekara-shekara domin ƙara wayar da kai kan darajar harshen Hausa, da kuma buƙatar bunƙasa shi a duk faɗin Duniya.

Abdulbaƙi Jari, wadda ya assasa Ranar Hausa ta Duniya

Hausa dai Harshe ne mai bunƙasa, wanda ya fito daga dogon tarihi na al’adun Hausawa. A halin yanzu ya tsallaka iyakokin ƙasashe, ya shiga makarantun zamani, kafafen sadarwa da kasuwanci, har ma ya zama harshen hulɗa a tsakanin al’ummomi daban-daban.

Wannan ne ya sa aka buƙaci ware rana ta musamman domin gudanar da taro da tattaunawa kan rawar harshen da kuma ƙalubalen da yake fuskanta.

A bana, bikin ya samu karɓuwa ta musamman a Garin Daura na Jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, in da aka gudanar da shi a cikin Fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, a ranar Talata 26 ga Agusta, 2025.

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya 2025.

Wannan karo ya kasance mai muhimmanci domin ya cika shekaru 10 da fara bikin.

Masarautar Daura tare da haɗin guiwar hukumomin da abin ya shafa ne suka ɗauki nauyin wannan biki, wanda ya tara jama’a daga sassa daban-daban. An gudanar da shagulgula da dama, ciki har da baje kolin al’adu, wasannin gargajiya, muƙaloli da tattaunawa kan harshen Hausa da makomarsa.

Taken bikin na wannan shekara shi ne: “Amfani da Harshen Hausa Domin Wanzar da Zaman Lafiya.” Wannan ya fito ne daga la’akari da matsalolin tsaro da ake fama da su a sassa daban-daban, inda aka jaddada muhimmancin amfani da harshen Hausa a matsayin hanyar haɗin kai da wanzar da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Baya ga wannan, an kuma gabatar da Littattafai da dama da suka shafi tarihi, Adabi, Tatsuniyoyi da al’adun Hausawa ga Mai Martaba Sarkin Daura, a matsayin gudunmowa domin ƙara bunƙasa harshen Hausa da adanawa ga tarihi. Wannan kyauta ta ƙara armashi da daraja ga bikin bana.

A taƙaice, bikin bana ya nuna cewa Ranar Hausa ta Duniya ba wai biki ne na tunawa kawai ba, illa dai wata dama ce ta haɗin kai, wayar da kai, da kuma ciyar da harshen Hausa gaba a matakin Duniya.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An