Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'ada

Yadda aka gudanar da bikin Kamun Kifi na Argungu

Rahoto – Salahuddeen Muhammad

Bikin Kamun Kifi na Argungu na daga cikin manyan bukukuwan al’adu da suka fi shahara a Najeriya da ma Afirka baki ɗaya.

Ana gudanar da shi a Garin Argungu da ke Jihar Kabi, da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. In da yake zama wata muhimmiyar alama ta tarihi, haɗin kai da kuma bunƙasar tattalin arziki.

A yayin da Masunta suka taru a bakin Kogin Matan-Fada, su na riƙe da fatsotsinsu don fafatawa domin kamo Kifi mafi girma a ranar ƙarshe ta Bikin Kamun Kifin Argungu a Jihar Kabi, Najeriya.

📷 Hoto: Sodiq Adelakun/Reuters

                    Asalin Bikin

An fara bikin ne a shekarar 1934 domin tunawa da sulhun zaman lafiya tsakanin Masarautar Argungu da Sakkwato. Wannan sulhu ya kawo ƙarshen rikice-rikice tsakanin ɓangarorin biyu, in da daga bisani aka mayar da Bikin Kamun Kifin wata hanya ta ƙarfafa zumunci da haɗin kan al’umma.

An fara gudanar da Bikin Kamun Kifi na Argungu a shekarar 1934, ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Sama, wanda a wancan lokaci shi ne Sarkin Argungu (mai mulkin gargajiya na Argungu).

📷 Hoto: Sodiq Adelakun/Reuters

Wannan biki ya zama alamar kawo ƙarshen dogon tarihi na kusan ƙarni guda na gaba da rashin aminci tsakanin al’ummar Argungu da kuma mafi girman mai iko a yankin a wancan lokaci — Sarkin Musulmi na Sakkwato, Hassan Dan-Mu’azu.

📷 Hoto: Sodiq Adelakun/Reuters

Tun daga wancan lokaci, bikin ya zama al’adar shekara-shekara da ke jawo dubban baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje.

Dubban mahalarta — ciki har da ƙananan Yara da Mata sun fafata, Haka nan, Masunta daga maƙwabtan ƙasashen Afirka ta Yamma, kamar Nijar, Chad da Togo, sun halarci gasar tare da takwarorinsu na Najeriya.

📷 Hoto: Sunday Alamba/Associated Press

Muhimmancin Kogin Matan Fada

Ana gudanar da babban ɓangaren gasar ne a Kogin Matan Fada da ke Argungu. Wannan Kogi na da matuƙar daraja ta fuskar al’adu da muhalli, har ma UNESCO ta sanya shi cikin jerin wuraren tarihi na Duniya saboda muhimmancinsa na al’adu.

A al’adance, ana rufe kogin tsawon shekara baki ɗaya domin bai wa Kifaye damar hayayyafa. Ana buɗe shi ne kawai a lokacin bikin, ƙarƙashin kulawar Sarkin Ruwa — mai kula da harkokin ruwa da dokokin gargajiya.

Yadda Ake Gudanar da Gasar

Gasar kamun kifin ita ce zuciyar bikin. Dubban Masunta kan shiga kogin lokaci guda, su na amfani da ababen Gargajiya kaɗai — kamar Fatsa da aka saƙa da hannu, Tulu, Kwale-Kwale na gargajiya da kuma kama Kifi da hannu.

Masunta sun ratsa kogin Matan Fada suna zaune a kan Koraye, in da za su yi amfani da hannayensu da Fatsa kaɗai wajen kamun a Kifi.
📷 Hoto: Sunday Alamba/Associated

An haramta amfani da kayan zamani domin a kiyaye asalin al’ada. Duk wanda ya kamo kifi mafi girma shi ne ke zama Zakara, ya na samun kyautar Kuɗi da karramawa.

Masunta na neman Kifaye a lokacin Bikin Kamun Kifi na Argungu.
📷 Hoto: Sunday Alamba/Associated

A lokutan baya, an samu Masunta da suka kamo Kifaye masu nauyi fiye da kilo 50, abin da ke jawo hankalin Duniya.

Masunci Abubakar Usman, ya ɗauki hankalin Duniya a Bikin Kamun Kifi na Argungu 2026, saboda kifin da ya kamo mai nauyin kilo 59, wanda ya fi kowanne a gasar. Wannan babban nasara ya ba shi damar samun Mota Saloon guda biyu da kuma kyautar kuɗi naira Miliyan ɗaya (kimanin dala 739).

Ba Kamun Kifi Kaɗai Ake Ba

Bikin Argungu ba gasar kamun Kifi kaɗai ba ce. Ya haɗa da:

  • Kokawar Gargajiya
  • Wasannin Dawaki
  • Kaɗe-kaɗe, Waƙe-waƙe da Raye-rayen al’adu
  • Nunin kayan gargajiya

Wannan ya sa bikin ya zama cikakken dandali na baje kolin al’adun Hausawa da Arewa baki ɗaya.

Tasirin Bikin ga Tattalin Arziki

Wasu masunta a yayin Bikin Kamun Kifin Argungu.
📷 Sunday Alamba/Associated Press

Bikin na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin yankin. A lokacin bikin:

  • Otal-otal da gidajen baki sukan cika maƙil
  • Ƴan kasuwa sukan samu riba mai yawa
  • Masunta sukan sayar da kifayen da suka kama
  • Matasa sukan samu ayyukan wucin-gadi

Wannan ya sa bikin ya zama wata muhimmiyar hanya ta inganta yawon buɗe ido da samar da kuɗaɗen shiga ga al’umma.

Dakatarwa da Dawowa

Saboda matsalolin tsaro da na ababen more rayuwa, an dakatar da bikin a shekarar 2010. An yi ƙoƙarin dawo da shi a 2020, sai dai ba a ci gaba ba.

A tsawon shekaru da dama, bikin ya bunƙasa ya koma ɗaya daga cikin manyan bukukuwan al’adu a Najeriya, ya na jan hankalin baƙi daga sassa daban-daban na Duniya. Sai dai matsalolin tsaro da ƙalubalen kuɗi sun sa ya daina gudana a kai a kai, ya koma ana shirya shi lokaci-lokaci. A cewar masu shirya taron, cikakken bikin na ƙarshe da aka gudanar ya gudana ne shekaru shida da suka gabata.

📷 Hoto: Sodiq Adelakun/Reuters

A baya-bayan nan, an sake farfaɗo da shi tare da halartar manyan jami’an Gwamnati ciki har da Shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, da Gwamanan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, da kuma Mai Martaba Sarkin Argungu Hussein Mukwashe. 📷 The Punch

Dawowar bikin na nuna yunƙurin dawo da kwanciyar hankali da kuma farfaɗo da martabar al’adu.

Bikin a Matsayin Alamar Haɗin Kai

Ga al’ummar Argungu da ma Najeriya, bikin na nufin fiye da wasanni. Alama ce ta:

  • Zaman lafiya
  • Sada zumunci
  • Haɗin kai
  • Alkinta tarihi
  • Kare al’adu
  • Kula da muhalli

Bikin Kamun Kifi na Argungu ya tabbatar da cewa al’ada na iya zama hanya ta haɗa jama’a, bunƙasa tattalin arziki, da kuma tallata Ƙasa a idon Duniya.

Wani Masunci ya na nuna kifin da ya kama a yayin Bikin Kamun Kifin.

📷 Hoto: Toyin Adedokun/AFP

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'ada

Bikin Guérewol na Ƙabilar Wodaabe a Jamhuriyar Nijar

Bikin Guérewol wata gasa ce ta al’adar neman aure da ake yi a kowace shekara tsakanin al’ummar Wodaabe Fula na
Al'ada

Shin Kayan Lefe Kyakkyawa ko Mummunar Al’ada Ce?

Abdulmutallib A. Abubakar malami a sashen nazarin aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Barno kuma mai sharhi kan