Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'amuran Yau Da Kullum

Mata Sun fi Maza Yawa a Manyan Makarantu a Duniya — UNESCO

Muhimman Bayanan Rahoton sun Haɗa da:

  • A shekarar 2024, akwai Mata 114 a manyan makarantu kan Maza 100 a Duniya baki ɗaya.
  • Samun daidaito tsakanin jinsi ta samu a kusan dukkan yankuna, sai dai yankin Hamadar Sahara.
  • Adadin ɗaliban manyan Makarantu a Duniya ya haura Miliyan 269, bayan ya kasance kusan miliyan 100 a shekarar 2000.
  • Duk da yawan Mata a Jami’oi, har yanzu ba su da rinjaye a matakan Digirin-digirgir (Doctorate) ko shugabancin cibiyoyin ilimi.
  • Yankin Hamadar Sahara na da mafi ƙarancin yawan shiga manyan Makarantu, in da kashi 9% kawai ke samun damar hakan.
  • Haka kuma, UNESCO ta nuna cewa ci gaban fasahar zamani da AI na sauya tsarin ilimi, amma jami’o’i kaɗan ne suke da cikakken tsarin AI a hukumance.

Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO, ta bayyana cewa, Mata yanzu sun fi Maza yawa a manyan Makarantu a Duniya, kamar yadda sabon rahotonta kan ilimi mai zurfi ya nuna.

Rahoton ya bayyana cewa a shekarar 2024, akwai Mata 114 a manyan Makarantu kan Maza 100 a Duniya baki ɗaya, alamar cewa Mata sun samu gagarumin ci gaba wajen shiga Jami’oi da sauran Cibiyoyin Ilimi mai zurfi.

UNESCO ta ce, yawan ɗaliban manyan Makarantu a Duniya ya ƙaru sosai cikin shekaru 20 da suka gabata, inda adadin ya tashi daga kusan Miliyan 100 a shekarar 2000 zuwa sama da Miliyan 269 a shekarar 2024. Wannan na nuna ƙaruwa da fiye da kaso 170% cikin 100% cikin shekaru biyu da suka gabata.

Rahoton ya nuna cewa, yankin Yammaci Turai da Arewacin Amurka na gaba wajen samun damar shiga manyan Makarantu, in da kusan kaso 80% cikin 100% na Matasa ke shiga Jami’oi ko kwalejojin ilimi mai zurfi. A Gabashi da Kudu maso Gabashin Asiya kuma, kaso ya kai kusan 67% cikin 100%.

Sai dai yankin Hamadar Sahara ne ke da mafi ƙarancin damar shiga manyan Makarantu, in da kaso 9% cikin 100% kacal na Matasa ke samun damar hakan, lamarin da UNESCO ta danganta da matsalolin tattalin arziki, ƙarancin cibiyoyin ilimi da kuma matsalolin tsaro a wasu ƙasashe.

Duk da cewa Mata sun fi yawa a Jami’oi, rahoton ya nuna cewa har yanzu Maza sun fi yawa a wasu fannonin karatu kamar Injiniya, Fasahar Sadarwa da Kimiyyar Na’ura (ICT), yayin da mata suka fi yawa a fannonin lafiya, ilimi da zamantakewa.

Haka kuma, UNESCO ta bayyana cewa, Mata har yanzu ba su da rinjaye a matakan Digirin Digirgir (PhD) da kuma shugabancin Jami’oi, in da suke riƙe da kusan kashi 30% cikin 100% na manyan muƙaman gudanarwa kawai.

Rahoton ya kuma yi nuni da yadda bunƙasar fasahar zamani da Ƙirƙirarriyar Basira (Artificial Intelligence) ke sauya tsarin ilimi a Duniya, in da UNESCO ta ce Jami’oi da dama ba su da cikakken tsari ko manufofi kan yadda za a amfani da AI wajen koyarwa da bincike.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

20 Comments

  1. Cameron4745

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/XWQul

  2. Cameron3453

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/eClZI

  3. Cleo1591

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/72z2v

  4. Hayden1379

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/REgXd

  5. Karl3850

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/ITqb3

  6. Marissa4209

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/zFhj7

  7. Alexander3720

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/9Taai

  8. Sophia4064

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/cBygw

  9. Aurora4610

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/slPSM

  10. Bryan415

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/MLBrv

  11. Ralph4270

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/UHRdz

  12. Jamal1641

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/3HgxU

  13. Lawrence3627

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/qd4Tq

  14. Faith101

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/h87Kl

  15. Chandler1730

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/jnFdp

  16. Autumn1685

    01/06/2026

    Новинки музыки 2026 скачать бесплатно https://shorturl.fm/7J6vJ

  17. Allison1887

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/IPY95

  18. Gabriella748

    01/06/2026

    Популярные песни 2026 скачать бесплатно https://shorturl.fm/dfuzp

  19. Alyssa4690

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/gDIHG

  20. Chuck2015

    01/06/2026

    https://shorturl.fm/D8nhZ

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An