Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!
Masarautar Katsinar Maraɗi, babbar Masarauta ce mai daɗaɗɗen tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajar Masarautar ta tashi daga Sarki zuwa Sultan. Daga: Awwal Ahmad Janyau Mafi yawancin al’ummar Masarautar Maraɗi Hausawa ne da kuma wasu ƙabilu na Nijar kuma ta ƙunshi Musulmi da kuma wasu kaɗan mabiya addinin Kirista. Masarautar Maraɗi ta yi iyaka da […]
Wannan shi ne karo na biyar a jere da William Masvinu ke lashe gasar mutumin da ya fi kowa muni ( Mr Ugly) a ƙasar, kuma ya ce nasarar ta ba shi damar yin fice da har yake samun kuɗaɗe daga tallace-tallace. A cewarsa, ya na alfahari da muninsa, kuma ya na son ya lashe […]
Sarauniya Pokou, ko Awura, Aura, ko Abla Pokou (ta yi sarauta c. 1750 – c. 1760) ita ce Sarauniya kuma ta kafa ƙabilar Baoule a Yammacin Afirka (Ivory Coast), yanzu Côte d’Ivoire, Ta yi sarauta a kan wani reshe na Daular Ashanti mai ƙarfi, yayin da yake faɗaɗa Yamma. Ƙabila ta al’ummar Akan, mutanen Baoule […]
Wata ƴar ƙasar Maroko mai sa Hijabi da aka samar da ita da Ƙirƙirarriyar Fasaha ta yi nasarar lashe Gasar Kyau ta Miss AI ta farko a Duniya. Macen Ƙirƙirarriyar Fasaha, wadda ta lashe Gasar Kyau ta Duniya. |Hoto: MM News Kenza Layli, mai faɗa a ji a shafukan sada zumunta kan salon rayuwa, ta […]
Wata ƙwararriyar mai zane-zanen fasaha ƴar ƙasar Azerbaijan mai shekaru 33, mai suna Tünzale Memmedzade, ta kasance mutum na farko a duniya da ta fara rubuta Al-kur’ani mai girma gaba ɗaya a jikin siliki. Memmezade, ta fara aikin ne bayan ta samu labarin cewar, a baya ba a taɓa rubuta Al-kur’ani da siliki ba. Littafin […]
An fara kisan kiyashi a Rwanda lokacin da aka harbo Jirgin Saman da ke ɗauke da Shugaban Rwanda Juvénal Habyarimana da shugaban Burundi Cyprien Ntaryamira. Daga: Muhammad Cisse A shekarar 1994 a cikin kwanaki 100 kacal, kisan kiyashin da aka yi a Ƙasar Ruwanda ya zama daya daga cikin manyan laifukan Yaƙi a Tarihin wannan […]
Bayan Juyin Mulkin da Iran ta yi a shekarar 1953, Pahlavi ya haɗa kai da Amurka da Ƙasashen Yamma don yin mulki da ƙarfi a matsayin cikakken Sarki. Ya dogara kacokan kan goyon bayan da Amurka ke samu don ya ci gaba da riƙe madafun ikon da ya riƙe na tsawon shekaru 26. A wannan […]
Yaƙin Basasar Syria (Sham) dai wani Yaƙin Basasa ne mai ɓangarori da dama a Ƙasar Syria da ake gwabzawa tsakanin Jamhuriyar Larabawa ta Syria ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasar Syria Bashar al-Assad da wasu dakaru na cikin gida da na waje da ke adawa da Gwamnatin Syria da kuma juna, ta fuskoki daban-daban. Fiye da […]
Hukumar kula da al’adu da illimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta ayyana Hawan Daba na Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, a matsayin guda daga cikin al’adu da ke da mahimmanci a Duniya. Daga: Salahuddeen Muhammad A bikin na Hawan Dawaki wanda aka fara tun ƙarni na 15 a Kano, Sarki, wanda shi ne […]
Wannan rubutu da ake karantawa zai ba mu ƙarin haske game da wannan gari na Katsina. Katsina, babbar Masarauta ce, kuma mai daɗaɗɗen tarihi. Ta na ɗaya daga cikin asalin garuruwan Ƙasar Hausa. Kafin zamowarta wannan babban birni da a yau ya zama Hedikwatar Jihar Katsina sannan kuma Fadar Masarautar Katsina. Ta taɓa zama a […]
Kowace shekara a ranar 9 ga Disamba, ita ce Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya. Ana amfani da ranar ce domin wayar da kan jama’a game da illar rashawa a matakai daban-daban na rayuwa. Har ila yau, ya na ƙarfafa jama’a su yi aiki da sababbin hanyoyin magance da nufin samun nasara […]
Manyan ƴan bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne ƴan jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace. Daga; Ɗanladi Haruna Kasancewar Hausa Harshe ne mai sauƙin fahimta gami da basirar da Allah Ya yi wa ƙabilar wajen aro wata kalmar daga wani yaren, su mayar da ita tamkar ƴar asali a cikin […]
Babu wani takamaiman lokacin da za a iya bugun ƙirji a ce shi ne lokacin da Musulunci ya iso Ƙasar Hausa (Fago da Usman, 2010). Kasancewar Ƙasar Hausa yanki ne mai dausayi; Yanki mai albarkatun ƙasa, yakan samu Fatake masu zuwa kasuwanci daga sassan Duniya. Mutanen da suka fi zuwa wannan yanki da nufin kasuwanci […]
Masana kimiyya sun soma kula da tsuntsuwar ne tun a shekarar 1956 a lokacin da take da shekaru biyar. Wata tsuntsuwa wadda masana kimiyya suka yi amanna cewa, ita ce mafi tsufa a Duniya ta saki Ƙwai, kamar yadda masana suka tabbatar. Hukumar Kula da Kifaye da Namun Dawa ta Amurka ta ɗauki hotonta a […]